• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekaru 2 Ke Nan Da Barkewar Rikici A Tsakanin Rasha Da Ukraine

by CGTN Hausa
2 years ago
Rasha

A ranar 24 ga wata ne za a cika shekaru 2 da barkewar rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. Yanzu sojojin kasashen 2 na cikin tsaka mai wuya. Kasashen Amurka da Turai suna shirin kakabawa Rasha sabbin takunkumi. Ya zuwa yanzu babu alamar kawo karshen rikicin. Akasarin ra’ayoyin kasa da kasa sun takaita babbar asarar da rikicin ya haifar, tare da yin tunani mai zurfi kan dalilin da ya haddasa barkewar rikicin, da kuma yin kira a tsagaita bude wuta.

Rikicin Rasha da Ukraine shi ne yaki mafi muni da ya barke a nahiyar Turai bayan yakin cacar baka. Bisa kididdigar da hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD ta fitar, a cikin shekaru biyu da suka gabata, yawan mutanen Rasha da Ukraine da suka mutu da jikkata ya kai sama da dubu 500 yayin da sama da ‘yan Ukraine miliyan 10 suka rasa matsugunansu. Barkewar rikicin ya haifar da hauhawar farashin makamashi da abinci a duniya, a wasu kasashen Afirka kuma, an gamu da matsalar karancin abinci.

  • Kasar Sin: Mutane Miliyan 474 Sun Yi Yawon Shakatawa A Yayin Hutun Bikin Bazara
  • An Buga Jadawalin Zagaye Na 16 Na Gasar Europa Da UEFA Conference League

Yayin da ake sake tunanin rikicin yanzu, an kara fahimtar cewa, siyasar kasa da kasa, ba abu mai sauki ba ne. Ra’ayin yakin cacar baki shi ne dalilin da ya haifar da rikicin. Amurka kuma tana yunkurin yin fito-na-fito. Haka kuma, sanya takunkumin kashi kai ba shi da amfani, illa rura wuta kawai.

Bugu da kari, wannan rikici da aka shafe tsawon shekaru biyu ana yi, ya kuma tabbatar da cewa takunkumin da aka sanya wa hannu bai yi tasiri ba, sai dai yana kara zafafa rigingimu da fadace-fadace. Kwarewar tarihi ta tabbatar da cewa karshen kowane rikici shi ne komawa teburin tattaunawa.

Yadda aka dauki tsawon lokaci ana rikici tsakanin Rasha da Ukraine, an kuma kara sarkakiyyar rikicin da fadada rikicin, bai dace da moriyar kasashen duniya ba. Ba yadda za a yi sai a yi tattaunawa da shawarwari. Tilas ne a yi adalci da kai zuciya nesa da nuna daidaito kan ikon mulkin kan Ukraine da tsaronta da kuma damuwar Rasha ta fuskar tsaro. (Tasallah Yuan)

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Kai Ziyarar Jaje A Zurmi Da Birnin Magaji

'Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Kai Ziyarar Jaje A Zurmi Da Birnin Magaji

LABARAI MASU NASABA

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.