Nijeriya na da dimbin wadatattun albarkatun kasa, sai dai, abin takaici, ragwanci da kasa katabus din shugabanninta wajen hako wadannan albarakatun kasar, ya sa kachokam, suna dogaro ne da fannin mai, a domin bunkasa tattalin arzikin kasar.
Rashin hako albarkatun kasar, ya sanya suna yin ikirarin cewar, suna da wadannan albarkatun ne kawai.
- Ofishin Jakadancin Faransa Da Hadin Gwiwar IITA Sun Horar Da Mata 500 Kasuwancin Noma
- Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Kudirin Kara Yawan Membobi Daga 360 Zuwa 366
Rashin hako albarkatun kasar, ya sanya ba a samun kudaden shigar da za a iya yin amfani da su, wajen inganta jin dadi da walwalar al’ummar kasar.
Abin takaici, a Nijeriya ta yau, ta kasance al’ummarta na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa saboda yawan samun almubazzaranci da dukiyar kasar.
Babu wata tantama maganar da ake yi Nijeriya ce, a gaba a cikin nahiyar Afirka da ake samar da mai, mai dimbin yawa, la’akari da yadda ake hako gangunan danyen mai kimanin miliyan 1.4 a kullum, sai dai, kuma wannan adadin, ya kai kasa da yawan kimanin miliyan biyu na gangunan man da ake hakowa a kullum.
A cikin wata 17 na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin ta yi ikirarin kirkiro da tsararan sauye-sauye, musamman ma a fannin samar da makamashi da kudaden musanya, domin ta zuba hannun jari a manyan fannonin ta na bunkasa tattalin arzikin kasa, musamman fannin samar da kayan aiki, kiwon lafiya, samar da wadatacciyar wutar lantarki da dai sauransu.
Kazalika, a yayin da wasu kasashen waje ke jinjinawa kokarin gwamnatin shugaban kasa Tinubu, musamman jinjinawar Asusun bayar da Lamuni da kuma Bankin Duniya (IMF).
Sai dai, duk da wannan yabawar tasu, a cikin gida Nijeriya, ‘yan kasar su kuma suna ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kaya wanda hakan ya kara jefa talakawan kasar, a cikin kangin talauci.
Koda yake, gwamnatin ta shelar daukar wasu matakai na ragewa talakawan kasar irin wannan zafin radadin talaucin, musamman ta hanyar turawa wasu talakawan kudi zuwa asusun su na ajiya a bankuna, amma, wannan tsarin, ba ya tafiya kamar yadda ya kamata.
Wasu kwararrun masana a kasar na ganin cewa, duba da cewa, kasar na da yanayi mai kyau, samun wadataccen ruwan sama, dausayi mai kyau, ya fi dacewa, a bai wa fannin aikin noma babban mahimmanci,a tuna da cewa, fannin shi ne, ginshikin bunakasa tattalin arzikin da kasar ta dogara da shi tun fil’azal.
Fannin aikin noma, shi ne wanda asali aka fi yin amfani da shi, a shekarun baya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda kuma shi ne, ya sa Nijeriya kasa mai arziki a cikin kasashen Afrika, a shekarun baya.
Bugu da kari kuma, fannin ya samu wannan dimbin nasarar ce, ta hanyar fitar da amfanin gona zuwa ketare wanda kuma ya ci gaba da tafiyar da tattalin arzikin kasar, bayan samun ‘yancin kai a 1960.
A wadancan shekarun baya, ba wata maganar yunwa, samun yaduwar cututtuka ko yunwa da sauransu.
Tun bayan da aka gano mai a shekarun baya, ba a yin amfani da albarkatun man domin a inganta rayuwar al’ummar kasar.
Dukiyar da ake samu daga albarkatun man, ta kasance ana kawai yin almubazzaranci da ita ne kawai, musamman yadda ake samun wasu jami’an gwamnati na tabka cin hanci da rashawa.
Wannan dabi’ar ta su, ta janyo ‘yan Nijeriya ba su amfana da albakarun da ake samarwa a fannin na man.
Bugu da kari, wannan lamarin sai kara kamari yake yi a Nijeriya, wanda duk da bugun Kirji da Nijeriya ke yi cewar, tana daya daga cikin kasashen duniya masu albarkatun mai.
Amma abin takaici, ‘yan kasar sai ci gaba suke yi da zama a cikin kangin talauci, rashin aikin yi, rashin samar masu da kayan more rayuwa, rashin hanyoyi masu kyau, wadatacciyar wutar lantarki da kuma kayan da za’a rika duba lafiyarsu.
Kazalika, fannin ilmin zamani shi ma ya tabarbare, wanda hakan ya janyo yara da dama, ba su zuwa makaranta, wadanda kuma ke zuwa makarantar, ba su samun ingantaccen ilimin.
A kwanan baya ne, Bankin Duniya ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da ta yi amfani da dukiyar kasar wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, duk da sauye-sauyen da Gwamnatin ta kirkiro da su, wadanda ta yi ikirarin, ta kirkiro da su ne, domin bunkasa tatattalin arzikin kasar.
Wannan shawarar ta Bakin duniya ta zo a kan gaba, in aka yi la’akari da cewa, dole ne shugabannin kasar, su mayar da hankali wajen inganta rayuwar ‘yan kasar, sama da nasu ra’ayin, kashin kansu.
Wannan Jaridar na da yakinin cewa, dole ne Gwamnatin mai ci, ta mayar da hankali wajen zuba hannun jari a manyan fannonin kasar, kamar, ilimin boko, kiwon lafiya da samar da kayan inganta rayuwar ‘yan kasar.
Bugu da kari kuma, akwai matukar bukatar samarwa fannin ilimin zamani wadatattun kudade tare da tabbatar da, ana biyan malamani ingantaccen albashi, musamman domin a dakile malaman da ke barin aikin koyarwa.
Fannin samar da kayan more rayuwa shi ma na bukatar kulawar da ta dace, saboda haka dole ne ta zuba hannun jari gyaran hanyoyi, samar da wadatacciyar wutar lantarki da kuma samar da tsaftatacce kuma ingantaccen ruwan sha.
Samar da wadattun kayan more rayuwar zai taimaka wajen kara habaka tattalin arzikin kasar wanda hakan zai janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari da samar da ayyukan yi.
Kwararru da dama, na da yakinin cewa, Bankin Duniya da Asusaun Bayar da Lamuni na Duniya, sun taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar tattalin arzikin Nijeriya.
A bisa tunanin mu, cin hanci da rashawa suna daga cikin dalilan da suka sanya ‘yan Nijeriya, ba su amfana da albarkatun kasar.
Bugu da kari, a bisa ra’ayin mu, dole ne Gwamnatin ta mayar da hankali wajen dakile cin hanci da rasahwa ta hanyar karfafawa hukumin kwarin guiwa da kuma kara jaddada doka domin a dakile dabi’arnan ta cin hanci da rashawa.
Alhakin gwamnati ne, gwamnatin ne ta tabbatar da cewa, duk wanda aka kama da dabi’ar cin hanci da rashawa, an hukunta shi kamar yadda dokar kasa ta tanadar domin hakan ya zama izina, ga sauran masu shirin aikata irin dabi’ar a nan gaba.
Abin so ne, Gwamnatin ta mayar da hankali a kan inganta fannoninta, kamar kiwon lafiya, ilimin zamani da samar da kayan ingantanta rayuwar al’umma.
Abin so ne, Gwamnatin ta samar da kyakyawan yanayi wanda zai ba wa ‘yan kasuwa na cikin gida damar bunkasa sana’ar su, wanda kuma samar da kyakyawan yanyin, na daya daga cikin hanyoyin da za iya jan hankalin masu son zuba hannun jari daga ketare.
Muna da cewa, yanzu ne ya kamata a fara yin hobbasa kuma dole ne Gwamnatin ta fara daukar matakai domin ‘yan kasar su amfana da albarkatun kasar da take da su.