ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Albarkatun Man Fetur Na Kasar Nan Na Amfanar Al’umma Kuwa?

by Leadership Hausa and Sulaiman
2 years ago
Man fetur

Nijeriya na da dimbin wadatattun albarkatun kasa, sai dai, abin takaici, ragwanci da kasa  katabus din shugabanninta wajen hako wadannan albarakatun kasar, ya sa kachokam, suna dogaro ne da fannin mai, a domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

 

Rashin hako albarkatun kasar, ya sanya suna yin ikirarin cewar, suna da wadannan albarkatun ne kawai.

ADVERTISEMENT
  • Ofishin Jakadancin Faransa Da Hadin Gwiwar IITA Sun Horar Da Mata 500 Kasuwancin Noma
  • Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Kudirin Kara Yawan Membobi Daga 360 Zuwa 366

Rashin hako albarkatun kasar, ya sanya ba a samun kudaden shigar da za a iya yin amfani da su, wajen inganta jin dadi da walwalar al’ummar kasar.

 

LABARAI MASU NASABA

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

Abin takaici, a Nijeriya ta yau, ta kasance al’ummarta na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa saboda yawan samun almubazzaranci da dukiyar kasar.

 

Babu wata tantama maganar da ake yi Nijeriya ce, a gaba a cikin nahiyar Afirka da ake samar da mai, mai dimbin yawa, la’akari da yadda ake hako gangunan danyen mai kimanin miliyan 1.4 a kullum, sai dai, kuma wannan adadin, ya kai kasa da yawan kimanin miliyan biyu na gangunan man da ake hakowa a kullum.

 

A cikin wata 17 na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin ta yi ikirarin kirkiro da tsararan sauye-sauye, musamman ma a fannin samar da makamashi da kudaden musanya, domin ta zuba hannun jari a manyan fannonin ta na bunkasa tattalin arzikin kasa, musamman fannin samar da kayan aiki, kiwon lafiya, samar da wadatacciyar wutar lantarki da  dai sauransu.

 

Kazalika, a yayin da wasu kasashen waje ke jinjinawa kokarin gwamnatin shugaban kasa Tinubu, musamman jinjinawar Asusun bayar da Lamuni da kuma Bankin Duniya (IMF).

 

Sai dai, duk da wannan yabawar tasu, a cikin gida Nijeriya, ‘yan kasar su kuma suna ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kaya wanda hakan ya kara jefa talakawan kasar, a cikin kangin talauci.

 

Koda yake, gwamnatin ta shelar daukar wasu matakai na ragewa talakawan kasar irin wannan zafin radadin talaucin, musamman ta hanyar turawa wasu talakawan kudi zuwa asusun su na ajiya a bankuna, amma, wannan tsarin, ba ya tafiya kamar yadda ya kamata.

 

Wasu kwararrun masana a kasar na ganin cewa, duba da cewa, kasar na da yanayi mai kyau, samun wadataccen ruwan sama, dausayi mai kyau, ya fi dacewa, a bai wa fannin aikin noma babban mahimmanci,a tuna da cewa, fannin shi ne, ginshikin bunakasa tattalin arzikin da kasar ta dogara da shi tun fil’azal.

 

Fannin  aikin noma, shi ne wanda asali aka fi yin amfani da shi, a shekarun baya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda kuma shi ne, ya sa Nijeriya kasa mai arziki a cikin kasashen Afrika, a shekarun baya.

 

Bugu da kari kuma, fannin ya  samu wannan dimbin nasarar ce, ta hanyar fitar da amfanin gona zuwa ketare wanda kuma ya ci gaba da tafiyar da tattalin arzikin kasar, bayan samun ‘yancin kai a 1960.

 

A wadancan shekarun baya, ba wata maganar yunwa, samun yaduwar cututtuka ko yunwa da sauransu.

 

Tun bayan da aka gano mai a shekarun baya, ba a yin amfani da albarkatun man domin a inganta rayuwar al’ummar kasar.

 

Dukiyar da ake samu daga albarkatun man, ta kasance ana kawai yin almubazzaranci da ita ne kawai, musamman yadda ake samun wasu jami’an gwamnati na tabka cin hanci da rashawa.

 

Wannan dabi’ar ta su, ta janyo ‘yan Nijeriya ba su amfana da albakarun da ake samarwa a fannin na man.

 

Bugu da kari, wannan lamarin sai kara kamari yake yi a Nijeriya, wanda duk da bugun Kirji da Nijeriya ke yi cewar, tana daya daga cikin kasashen duniya masu albarkatun  mai.

 

Amma abin takaici, ‘yan kasar sai ci gaba suke yi da zama a cikin kangin talauci, rashin aikin yi, rashin samar masu da kayan more rayuwa, rashin hanyoyi masu kyau, wadatacciyar wutar lantarki da kuma kayan da za’a rika duba lafiyarsu.

 

Kazalika, fannin ilmin zamani shi ma ya tabarbare, wanda hakan ya janyo yara da dama, ba su zuwa makaranta, wadanda kuma ke zuwa makarantar, ba su samun ingantaccen ilimin.

 

A kwanan baya ne, Bankin Duniya ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da ta yi amfani da dukiyar kasar wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, duk da sauye-sauyen da Gwamnatin ta kirkiro da su, wadanda ta yi ikirarin, ta kirkiro da su ne, domin bunkasa tatattalin arzikin kasar.

 

Wannan shawarar ta Bakin duniya ta zo a kan gaba, in aka yi la’akari da cewa, dole ne shugabannin kasar, su mayar da hankali wajen inganta rayuwar ‘yan kasar, sama da nasu ra’ayin,  kashin kansu.

 

Wannan Jaridar na da yakinin cewa, dole ne Gwamnatin mai ci, ta mayar da hankali wajen zuba hannun jari a manyan fannonin kasar, kamar, ilimin boko, kiwon lafiya da samar da kayan inganta rayuwar ‘yan kasar.

 

Bugu da kari kuma, akwai matukar bukatar samarwa  fannin ilimin zamani wadatattun kudade tare da tabbatar da, ana biyan malamani ingantaccen albashi, musamman domin a dakile malaman da ke barin aikin koyarwa.

 

Fannin samar da kayan more rayuwa shi ma na bukatar kulawar da ta dace, saboda haka dole ne ta zuba hannun jari gyaran hanyoyi, samar da wadatacciyar wutar lantarki da kuma samar da tsaftatacce kuma ingantaccen ruwan sha.

 

Samar da wadattun kayan more rayuwar zai taimaka wajen kara habaka tattalin arzikin kasar wanda hakan zai janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari da samar da ayyukan yi.

 

Kwararru da dama, na da yakinin cewa, Bankin Duniya da Asusaun Bayar da Lamuni na Duniya, sun taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar tattalin arzikin Nijeriya.

 

A bisa tunanin mu, cin hanci da rashawa suna  daga cikin dalilan da suka sanya ‘yan Nijeriya, ba su amfana da albarkatun kasar.

 

Bugu da kari, a bisa ra’ayin mu, dole ne Gwamnatin ta mayar da hankali wajen dakile cin hanci da rasahwa ta hanyar karfafawa hukumin kwarin guiwa da kuma kara jaddada doka domin a dakile dabi’arnan ta cin hanci da rashawa.

 

Alhakin gwamnati ne,  gwamnatin ne ta tabbatar da cewa, duk wanda aka kama da dabi’ar cin hanci da rashawa, an hukunta shi kamar yadda dokar kasa ta tanadar domin hakan ya zama izina, ga sauran masu shirin aikata irin dabi’ar a nan gaba.

 

Abin so ne, Gwamnatin ta mayar da hankali a kan inganta fannoninta, kamar kiwon lafiya, ilimin zamani da samar da kayan ingantanta rayuwar al’umma.

 

Abin so ne, Gwamnatin ta samar da kyakyawan yanayi wanda zai ba wa ‘yan kasuwa na cikin gida damar bunkasa sana’ar su, wanda kuma samar da kyakyawan yanyin, na daya daga cikin hanyoyin da za iya jan hankalin masu son zuba hannun jari daga ketare.

 

Muna da  cewa, yanzu ne ya kamata a fara yin hobbasa kuma dole ne Gwamnatin ta fara daukar matakai domin ‘yan kasar su amfana da albarkatun kasar da take da su.

Man fetur
Leadership Hausa
Website |  + posts Bio
  • Leadership Hausa
    Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
Man fetur
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Daƙile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wadanda Aka Sace A Zamfara Da Katsina
  • Sulaiman
    Guguwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum Huɗu, Ta Yi Mummunar Ɓarna A Sokoto
  • Sulaiman
    Mutum Ɗaya Ya Mutu, Sama Da 30 Sun Ɓace A Hatsarin Kwale-kwale A Jigawa
  • Sulaiman
    Badaƙalar Binciken Hukumar Bogi: Gbajabiamila Ya Gurfana Gaban ICPC

MASU ALAKA

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
Ra'ayinmu

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

July 3, 2026
sikila
Ra'ayinmu

Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya

June 26, 2026
Next Post
Mahaifin Da Ya Kashe Jiririnsa Ɗan Kwana 3 Ya Shiga Hannun Ƴansanda

Mahaifin Da Ya Kashe Jiririnsa Ɗan Kwana 3 Ya Shiga Hannun Ƴansanda

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wadanda Aka Sace A Zamfara Da Katsina

Sojoji Sun Daƙile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wadanda Aka Sace A Zamfara Da Katsina

July 21, 2026
nema

Guguwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum Huɗu, Ta Yi Mummunar Ɓarna A Sokoto

July 21, 2026
Hadarin Kwale-Kwale

Mutum Ɗaya Ya Mutu, Sama Da 30 Sun Ɓace A Hatsarin Kwale-kwale A Jigawa

July 21, 2026
ICPC

Badaƙalar Binciken Hukumar Bogi: Gbajabiamila Ya Gurfana Gaban ICPC

July 21, 2026
Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

July 20, 2026
Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

July 20, 2026
Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

July 20, 2026
NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

July 20, 2026
Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

July 20, 2026
Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

July 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.