Umar A Hunkuyi" />

Shin Buhari Ya Watsar Da Magu Ne?

…Duk Da Majalisa Ta Amince Ma Sa Da Nade-nade 207

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sami amincewar majalisar Dattijai a kan tabbatar da mutane 207 da ya nada a bisa mukamai daban-daban a cikin shekara guda da ta gabata.
Nade-naden mutane 207 da shugaban kasan ya yi sun hada da Alkalai, Ministoci, Jakadu, Kwamishinoni da shugabannin wasu hukumomin gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma a duk wadannan nade-naden da shugaban kasan ya yi, sam bai kawo sunan sake nada mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, domin a tabbatar masa da shugabancin hukumar ba.
Tun dai a ranar 9 ga watan Nuwamba na shekarar 2015 ce shugaban kasan ya nada Magu a matsayin shugaban hukumar, wanda kuma ake ta kai ruwa-rana da majalisar Dattijai ta wancan lokacin a inda majalisar ta ki ta amince da tabbatar da nadin na shi, tun a lokacin ne kuma yake ci gaba da jagorantar hukumar a matsayin rikon kwarya.
Sau biyu shugaban kasan yana aikewa da sunansa zuwa majalisar Dattijan ta 8 a karkashin shugabanta na wancan lokacin, Dakta Bukola Saraki, domin neman amincewar majalisar, amma kasantuwar wasu rahotannin da suka shafi tsaro daga hukumar DSS sai ya kasance bai iya samun amincewar majalisar ba. Amma dai ya ci gaba da zama a matsayin shugaban rikon kwarya na hukumar.
Sai dai tun daga lokacin da aka kaddamar da wannan sabuwar majalisar Dattijan ta 9 wacce ke karkashin shugabancin Ahmad Lawan, a ranar 11 ga watan Afrilu, 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aike da sunayen mutane 200 zuwa majalisar ta Dattijai wadanda yake neman majalisar ta tabbatar da nadin da yay i masu a bisa mukamai caban-daban, amma sam babu sunan Magun a cikin sunayen.
Hakan duk kuwa da tabbacin da Lawan ya bayar na cewa majalisar Dattijan ba za ta bata lokaci ba wajen tabbatar da nadin Magu din da zaran sashen shugaban kasan ya gabatar da sunansa ga majalisar domin amincewa.
A lokacin da shugaban kwamitin bai wa shugaban kasa shawara a kan yaki da cin hanci da karban rashawa, Itse Sagay, ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke zauren majalisar a Abuja, a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2019, Lawan ya shaida masa cewa sashen shugaban kasan bai aiko ma da majalisar wata bukata ta tabbatar da nadin Magun ba.
Majalisar Dattijan ta 9 wacce ke tinkaho da cewa ita abokiyar tafiyar sashen shugaban kasan ne wacce ke a shirye da ta karba tare da tabbatar da duk wanda shugaban kasan ya aike mata da nadinsa a kan kowane irin mukami ne, tun daga lokacin hawanta mutum guda daya ne kacal shugaban kasan ya aike mata da bukatar nada shi a kan wani mukami wanda kuma majalisar ta ki amincewa da nadin na shi a cikin shekara guda da ta gabata, ita ma din majalisar ta ki amincewa da nadin nata ne domin ta ki ta halarci majalisar domin a tantance ta.

Exit mobile version