Rukunin kamfanonin Dangote ya yi wani ƙarin haske game da rahotannin da suka nuna cewa matatar Dangote ta sanar da samun kashi 60% na man fetur da take buƙata daga NNPC, tare da kawar da duk wata fahimta ta rashin jituwa tsakanin ta da kamfanin.
Kamfanin ya jaddada cewa bai taba zargin NNPC da kasa samar musu da ɗanyen mai ba. Maimakon haka, damuwar su ita ce rashin aiwatar da wajibcin samar da ɗanyen mai na cikin gida daga hukumar kula da harkokin man Fetur ta ƙasa (NUPRC), wanda ya sa matatar man ke kasa samun cikakken buƙatarta na ɗanyen mai daga NNPC da Kamfanonin Mai na Duniya (IOCs).
- Dangote Da BUA Za Su Bayyana A Gaban Majalisa Kan Badakalar Haraji
- Masu Shigo Da Mai Za Su Kawowa Matatar Dangote Cikas – Obasanjo
Domin a watan Satumba, matatar Dangote ta buƙaci ɗanyen mai har manyan jiragen ruwa guda 15, amma NNPC ta ba da guda shida kawai. Duk da roko ga NUPRC, sauran jiragen ba a samu ba.
Lokacin da matatar ta tuntuɓi IOCs da ke aiki a Nijeriya, an tura ta zuwa sassan kasuwancin su na duniya. Saboda haka, matatar man ta kan sayi ɗanyen mai na Nijeriya daga ‘yan kasuwar duniya da ƙarin dala 3 zuwa 4 kowanne ganga, wanda ke kara farashin kowanne jirgi da dala miliyan 3 zuwa 4.
Rukunin kamfanonin Dangote ya sake jaddada kira ga NUPRC da ta cika wajibcin samar da ɗanyen mai na cikin gida kamar yadda dokar masana’antar mai ta kasa (PIA) ta tanada.