Ni ban san ma ina shugabanni Kungiyar Daliban Jami’o’in ta Kasa (NANS) da na jihohi suka shiga tun a lokacin da aka fara yajin aikin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya.
Shin suna ma raye kuwa? Shin suna ma da wakilai a cikin kwamitin da ake zaman tattaunawa tsakanin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da Gwamnatin tarayya?
- Sai Mun Yi Gwajin Miyagun Kwayoyi Kafin Daura Aure A Abuja – NDLEA
- APC Ta Dunkule Kan Tinubu, PDP Na Kokarin Sulhu Da Wike
Idan suna da su, ina su ke? Mai suka ce? Idan ba su da wakilai a zaman. To mai ya sa? Dole ya kamata a ce dalibai na da wakilci cikin zaman, domin lamarin ya shafe bangarori uku ne; ASUU, Gwamnatin Tarayya da kuma dalibai, saboda haka ya kamata kowa na da wakilci a zaman.
Gwamnati da wakilai dalibai kowa ya mallaki duk takardun bukatun ASUU, ta nan ne su daliban za su fahimci ina aka nufa.
Mai gwamnati ta ce za ta yi, mai ta ce ba za ta yi ba. Amma matukar dalibai basu da wakilai a cikin zaman, to cikin duhu za su kasance ko da yaushe. Domin ko an janye yajin aikin za a sa ke komawa.
Domin bana ganin kaman shugabannin kungiyar dalibai na taimaka wa daliban yadda ya kamata domin kawo karshen wannan yajin aikin na ASUU.
Matakai da shugabannin kungiyar daliban suke dauka bai gamsar da ni kamar suna yi wa daliban shugabanci yadda ya kamata ba.
Kamata ya yi yadda mu ke ganin shugabannin ASUU da na Gwamnatin Tarayya kullum cikin gidan talabijin da jaridu, su ma a dinga ganin su haka muna jin inda suka dosa da sauransu kan lamarin.
Domin su za su matsa wa ASUU da gwamnati su yi abin da ya kamata. Idan kai da abu ya shafe ka kai tsaye baka nuna ka damu ba, to ina kuma ga wani daban?
Wannan yajin aikin ASUU ba wanda bai shafa ba, amma kai tsaye ta fi shafar daliban Jami’a. Saboda haka su ya kamata a fi jin su a ko da yaushe, amma shiru kake ji.
Na fahimci da ASUU da gwamnati kowa na da maganar banza a bakin shi. Idan fa har da gaske suke yi, to dole ASUU da gwamnati su daina fitowa suna jefa wa juna maganganun banza wanda bai dace ba. Sannan su daina fito da abin da da suka tattauna a zaman da suke yi har sai sun samu matsaya.
Saboda ‘yan jaridu da wadansu mutane na kara rura wutar yakin da ke tsakanin ASUU da gwamnati.
Su kuma shugabannin kungiyar daliban jami’a kamar ba sa raye a duniya. Dole su ma za su matsa wa ASUU da gwamnati su yi abin da ya kamata. Idan ba su da wakilai a zaman da ake yi, su nema dole suma a sa su cikin zaman.