Gontanamo dai wani sansani ne na sojojin Amurka da yake a Kasar Kyuba, kuma shi kadai ne sansanin sojojin Amurka a wata Kasa Mai bin tsarin kwaminisanci.
Shi dai wannan sansani yana Kudu maso Yammacin Kasar ta Kyuba, kusan tafiyar mil 400 daga garin Miyami, kuma sama da mutanen Kasar Amurka kimanin 3000 ne a wannan sansani, wadanda suka hada da sojoji da farar hula da kuma iyalansu.
Wannan sansani ya samo asali ne daga tarihin tsohon tsarin sansanonin Amurka a Kasashen Duniya. Tsarawa da kuma sanya wannan sansani a Kasar Kyuba ya faru ne tun lokacin da akai yaki tsakanin Kasar Amurka da Kasar Spaniya, lokacin da sojojin Amurka suka samu galaba akan sojojin Spaniya na rundunar “Caribbean’’ a kusa da garin Santiago da ke Kasar Kyuba a shekarar 1898.
A shekarar 1903 ne dai Kasar Amurka ta karbi hayar yankin daga Kasar Kyuba domin amfani da shi a matsayin tashar shan mai ga rundunar sojojinta na ruwa, amma a shekarar 1934 wa’adin yarjejeniyar da Kasashen biyu suka yi ya cika.
A lokacin da shugaban Kasar Amurka Eisenhower ya yanke huldar jakadanci da Kasar Kyuba a shekarar 1961, sai dubban ’yan gudun hijira na Kasar Kyuba suka cika sansanin. Kai da shekara ta zagayo ma sai jami’an sojan Kasar ta Kyuba su kai kaura zuwa sansanin na watanni da dama, a lokacin rikici akan makamai masu linzami na Kasar ta kyuba.
A shekara ta 1964 sansanin sojojin ruwan akan dole ya zama mai dogaro da kansa bayan shugaba Fidel Castro ya yanke wa sansanin wutar lantarki da kuma ruwan sha.
A shekarar 1991 sansanin ya zama wani masauki na wucin gadi ga dubban masu kaura daga Kasar Haiti, wadanda suka gudu domin tsoron juyin mulkin sojoji a kasar. Haka zalika a shekarar 1994 an yi wa wasu makauratan kimanin su 45,000 daga Cuba da Haiti masauki na wucingadi a wannan sansani.
Kamar yadda bayanai suka nunar daga Kasar ta Amurka, babban burin wannan sansani shi ne, ya kasance a matsayin wani sansani na samar da kayayyakin aiki ga rundunar sojojin ruwa na yakin Caribbean jiddan walahairan suna sintiri a kewayen sansanin.
To tuni dai sansanin na Guantanamo Bay ya dawo cikin labarun yau kullum, kuma a farkon shekara ta 2002 ne aka gina wani kurkuku a sansanin da ya haifar da kace-na ce a halin yanzu, wanda a ke kira da Turanci (Camp D-Ray) in da ake tsare da musulmi ’yan gwagwarmaya musamman ma wadanda ake zarginsu da alaka da kungiyar Al-Ka’ida da Taliban.
Tarzoma a kurkukun guantanamo
Wasu masu gadin kurkukun soji na tsibirin Guantanamo sun yi ta harbe- harbe da harsashen roba don kwantar da tarzomar da ta barke a gidan kurkukun.
Tarzomar ta abku ne lokacin da ake kokarin mai da fursunonin dakunan da ake tsare da su.
Jami’ai a gidan kurkukun na gwamnatin Amurka dake Cuba sun ce wasu fursunoni ne suka yi amfani da wasu makamai da suka harhada don hana komawa da su cikin dakunansu.
Zaman dar-dar ya karu a gidan kurkukun sakamakon yajin kin cin abinci da wasu fursunonin suka fara tun a watan Fabrairu, bayan da wasu fursunoni suka zargi masu gadinsu da bincika Kur’anan da suke amfani da su kan ko suna dauke da wasu abubuwa da aka haramta.
Jami’an gidan kurkukun na Guantanamo sun ce fursuna guda ne kawai ya samu raunuka lokacin tarzomar.
Kungiyoyin Kare Hakkin bil-‘Adama da lauyoyi sun ce, wannan na faruwa ne sakamakon gazawar da hukumomin suka yi wajen yanke shawarar yadda za su tafiyar da fursunonin, da akasarin su sun shafe fiye da shekaru goma.
Bayanai dai sun ce Jami’an gwamnatin Amurka sun riga sun ba da umarnin a saki kimanin casa’in daga cikin fursunonin, amma kuma har yanzu ana ci gaba da rike.
Wannan kuwa na faruwa ne sakamakon wasu dalilai da suka shafi ka’idojin fitar da su daga gidan kurkukun, da kuma tunanin yiwuwar musguna musu bayan an maishe su kasashensu.
Yawan fursunonin da ke yajin kin cin abinci a guantanamo ya kai 100
Yawan fursunonin da ke yajin kin cin abinci a gidan kurkukun ihunka banza da Amurka ta kafa a tsibirin Guantanamo sun kai 100 daga cikin 166 da ake tsare da su a halin yanzu.
Tun a ranar 6 ga watan Fabarairun da ya gabata ne dai fursunonin suka soma yajin kin cin abinci, kuma 20 daga cikinsu na a cikin mawuyacin hali, inda tuni hukumomin gidan yarin suka soma yi masu duren abinci ta hanyar saka masu wani bututu da ke isa a uwar hanjinsu.
Laftal-kanar Samuel House, daya daga cikin manyan jami’an gidan yarin na Guantanamo, ya ce yanzu haka akwai wasu fursunoni biyar da aka kwantar a asibiti sakamakon yadda suka tagayyara.
Su dai wadannan fursunoni sun shiga yajin kin cin abinci ne domin nuna rashin amincewarsu dangane da yadda ake tsare da su ba tare da an gurfanar da su a gaban alkali ba.