Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Shin Ko Tarayyar Turai Za Ta Iya Kaucewa Zama ’Yar amshin Shatar Amurka?

Published

on

Shin ko Tarayyar Turai za ta iya kaucewa zama ’yar amshin shatar Amurka?

A baya bayan nan, cikin muhimman abubuwan dake jan hankalin duniya, akwai batun yadda Amurka ke matsa kaimi, wajen kafawa kasar Sin kahon zuka daga dukkanin fannoni.
Mahukuntan Amurka, da ’yan siyasar kasar na ta furta kalamai na zargi da nuna adawa da manufofin kasar Sin, ba tare da gabatar da wasu hujjoji ba.
Ga misali a ranar 1 ga watan nan na Yulin nan, sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, ya dora bisa suka ba kakkautawa da yake yiwa kasar Sin, inda yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar White House, ya yi kira ga kasashe mambobin tarayyar Turai ta EU, da su goyi bayan Amurka, kan duk wasu manufofi da suka jibanci kasar Sin.
A makon da ya gabata ma, ya aike da wani sako ta kafar bidiyo ga taron Copenhagen na kasashen Turai, inda ya ce kasar Sin ce ta tilastawa Amurka daukar dukkanin matakan da ake gani a halin yanzu. Har ma yake cewa, matakan na Amurka, adawa ce tsakanin ’yanci da salon danniya, kuma Amurka na da al’adu iri daya da Turai.
Hakika dai kalaman Pompeo ba su da tushe ko makama. Illa dai kawai wasu makamai ne na yakin cacar baka da yake amfani da su, wajen tursasawa kasashen Turai karbar tunani da mahangar Amurka, ta yadda daga karshe, hakan zai ingiza turan fadawa tarkon nunawa wasu sassa duniya wariya da kyama.
Duk da cewa Turai na da tsare-tsarenta mabanbanta da na sauran sassan duniya, amma kuma hakan ba ya nuna cewa, wajibi sai ta zamo ’yar amshin shatan Amurka. Kuma a zahiri take cewa, gwamnatin shugaba Trump ba ta martaba manufofin ci gaban Turai. Shaidu sun tabbatar da cewa, Amurka ba ta dauki Turai a matsayin abokiyar tafiya ba, maimakon hakan tana daukar kasashen nahiyar a matsayin ’yan korenta, da ya wajaba su yi biyayya ga manufofin ta sau da kafa.
Ana iya fahimtar hakan, idan an duba wasu muhimman al’amura da suka wakana a baya bayan nan. Misali Amurka ba ta martaba kudurin Turai na yin biyayya ga yarjejeniyar makamai ta Iran ba. Amurka ta kuma tursasa Turai, wajen amincewa da takunkumai da dama da ta kakabawa sassan kasashen duniya, ba tare da la’akari da dokokin kasa da kasa ba.
A daya bangaren kuma, Amurka karkashin shugabancin gwamnatin Trump, ta sha nuna adawa da kasuwar bai daya ta Turai, wadda yake kallo a matsayin barazana ga sashin kasuwancin Amurka, matakin da ya kai ga dorawa Turai karin harajin cinikayya a wasu sassa. Ko da a baya bayan nan ma, sai da Trump ya zargi kasar Jamus da cin kazamar riba kan Amurka, yayin da sassan biyu ke hada hadar cinikayya.
Bugu da kari, gwamnatin Trump ta janye daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa mai helkwata a Hague, kotun da Mr. Pompeo ya kira da “ta jeka na yika”. Yana mai cewa kotun ba ta da wani hurumi na hana Amurka aiwatar da ikonta na mulkin kai. Tuni kuma wannan mataki ya ci karo da adawa daga daukacin shugabannin kasashen Turai.
Kari kan hakan, Amurka ta shiga takun saka da Turai, inda ta kai ga ficewarta daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. Har wa yau Amurka, ta ci gaba goyon bayan mamayar da Isra’ila ke yiwa yankunan Falasdinawa, duk kuwa da adawar da ragowar nahiyoyin duniya ke yi ga wannan manufa. To kuwa idan har da wadannan banbance-banbancen ra’ayi, da sabani tsakanin Amurka da Turai, me ya sa Mr. Pompeo ya dage cewa lallai sai Turai ta goyi bayan Amurka, game da batutuwan da suka shafi kasar Sin?
Lokaci ne kadai zai tabbatar da ko kasashen na Turai za su yi hangen nesa, wajen kaucewa fadawa tarkon Amurka, na mayar da su ’yan amshin shata, ko kuma za su rungumi junansu, tare da ci gaba da cudanya da sauran sassan duniya, ta yadda za su more ribar hadin kai, tare da gudu tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)
Advertisement

labarai