Yayin da kungiya irin ta Real Madrid ke tunkaho da zaratan ‘yanwasan gaba hudu da suka hada da Kylian Mbappe da Jude Bellingham da Binicius Jr da kuma Rodrygo, wadanda ka iya dama lissafin duk wata kungiya da ta yi karo da ita, shin kungiya irin Liberpool ya za ta kasance idan yau ba ta tare da tauraron dan gabanta Mohamed Salah ba? Wanda shi ne jagoran kungiyar a yanzu.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ka iya dogaro da kowanne daga cikin zaratan nata hudu a ranar da take cikin bukata kuma ya fitar da ita kunya, kamar yadda Mbappe ya ci kwallo uku da ya sallami Manchester City (6-3 jimilla gida da waje) ya kuma kai kungiyarsa matakin kungiyoyi 16 na gasar Zakarun Turai a ranar Laraba a filin wasa na Estadio Santiago Bernabeu.
- Kasar Philippines Za Ta Dandana Kudarta Game Da Gudummawar Soja Da Amurka Ta Ba Ta
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji Kan Kayayyakinta
Wannan tambaya da ake yi kan Liberpool idan ba ta tare da Salah ta kara bayyana bayan karawar kungiyar a gidan Aston Billa inda suka yi canjaras 2-2. Tauraron na Masar ne ya fara daga raga a karawar ta Laraba inda a minti na 29 ya ci wa Liberpool kwallo da taimakon Diogo Jota, kafin kuma Y. Tielemans ya farke a minti na 38 wannan kuwa duk da cewa ba ya kan ganiyarsa a wasan na ranar Laraba.
Sai kuma O. Watkins ya sa Aston Billa a gaba ana shirin tafiya hutun rabin lokaci da kwallo ta biyu, wadda kuma T. Aledander-Arnold ya farke wa Liberpool a minti na 61 da taimakon Salah. kwallon da Salah ya ci da kuma wadda ya bayar aka farke sun sa a yanzu yana da kwallo 39 da yake da hannu a ciki a wannan kakar a Premier a bana – inda ya ci kwallo 24 ya kuma taimaka aka zura guda 15.
Haka kuma da wadannan alkaluma Salah din ya zama danwasa na biyar da ya ci kwallo fiye da 15 ya kuma bayar da taimako aka ci 15 a Premier a bana, inda ya shiga rukunin su Eric Cantona, da Matt le Tissier, da Thierry Henry da kuma Eden Hazard, kuma shi har yanzu yana ci gaba da buga wasa wanda hakan yake nufin zai iya kafa sabon wani tarihin kafin karshen kakar wasa ta bana.
Salah ya kasance danwasa na farko a gasar Premier da ya ci ya kuma bayar aka ci a wasanni daban-daban har goma a kaka daya. Sannan shi ne danwasa na farko da ya yi haka a daya daga cikin manyan gasar Turai biyar tun bayan Lionel Messi da ya yi wannan bajinta a kakar 2014-15, inda ya yi wa Barcelona hakan da kwallo 11.
Sai dai babban abin da yake gaban kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ko kuma yake ci mata tuwo a kwarya shi ne kasancewar a karshen wannan kakar kwantiragin Muhammad Salah zai kare kuma har kawo yanzu bai sake sabon kwantiragin ba, tunda har yanzu ba su cimma wata yatrjejeniya ba wadda za ta saka ya ci gaba da zama a kungiyar ta Liberpool.
Mai koyuar da ‘yan wasan kungiyar, Arne Slot ya ce kwazon da Mohamed Salah ke yi a wasannin bana, zai kara yin tsada idan Liberpool za ta tsawaita kwantiraginsa kuma dan wasan na tawagar Masar zai cika shekara 33 da haihuwa cikin watan Yuni lokacin da yarjejeniyarsa za ta kare da kungiyar ta Liberpool wadda take buga wasanninta a katafaren filin wasa na Anfield.
To sai dai dan wasan, yana taka rawar gani a kakar nan fiye da bajintar da ya yi a kungiyar a kakar wasa ta 2017 domin shine ya karbi kyautar fitatcen dan wasa a karawar da Liberpool ta doke Manchester City 2-0 ranar Lahadi a Etihad a Premier League kuma hakan ne ya sa Liberpool ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki 11 tsakani da Arsenal ta biyu da tazarar maki 20 tsakani da Manchester City ta hudu.
Muhammad Salah ya ci kwallo 30 a kakar nan 25 daga ciki a Premier League, na farko da yake da hannu a cin kwallo 40 ko fiye da haka a kaka biyu a babbar gasar ta Ingila. Haka kuma shi ne kan gaba mai hannu a cin kwallo 50 a dukkan karawa a bana tsakanin manyan gasar Turai biyar da suka hada da Premier ta Ingila da La liga da Seria A da Lig 1 na faransa da Bundes Liga ta Jamus.
Liberpool tana da wani tsari da take taka tsantsan kan tsawaita yarjejeniya da duk wani dan wasanta da ya kai shekara 30 da haihuwa kuma hakan ne yasa shima dan wasa Birgil Ban Dijk har yanzu kungiyar bata kara masa sabon kwantiragi ba tare da dan wasa Trend Aledandre Arnold dan Ingila, wanda tuni kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shiga tattaunawa da shi domin ya koma kasar Spaniya da buga wasa.
Liberpool, wadda take jan ragamar teburin Premier League ta karbi bakunci kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United a ranar Laraba a gasar Premier kuma daga nan za ta je ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League ranar Laraba 5 ga watan Maris.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp