Shin A Na Iya Tayar Da Wanda Ya Mutu?

A wani rahoto da kafar yada labarai ta BBC sashen hausa ta nakalto, ta yi bayani sanka-sanka dangane da maudu’in nan mai sarkakiya. Inda aka kawo dogon bayani mai cike da misalai.

Fahimtar al’amuran mutuwa za su taimaka wa kwararru wajen dakatarwa da farfado da matattu da ke da kalubale.

Zach Conrad ya mutu a Philadelphia a ranar 3 ga Yunin 2012. A ranar, Conrad wanda masanin hada-hadar kudi ne mai shekara 36 na cikin annashuwa, kuma ya hau kekensa yana kewaya shi kadai kamar yadda ya saba a kwanakin karshen mako. Cikin zagayen nasa, sai Conrad ya fahimci akwai matsala. Tsayawarsa ke da wuya, sai ya fadi a kasa kwaraf. Zuciyarsa ta daina bugawa har ya daina numfashi. Ciwon bugun zuciya ne ya same shi.

A kowace shekara, kimanin mutum 300,000 a Amurka kan yi fama da ciwon bugun zuciya. Mafi yawansu kan mutu kai tsaye; kuma kashi 80 zuwa 90 na wadanda suka karke a asibiti na mutuwa.

Ba da saninsa ba, Conrad zai shiga ayarin masu kalubalantar fahimtarmu game da mutuwa. A wasu al’ummomin, daga kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na masu fama da ciwon bugun ciwon zuciya kan bar asibiti a raye. Ana kyautata zaton cewa ‘yan kadan da suka yi nasarar rayuwa suna kwanciya ne a asibitin da ke aiwatar da managartan dabarun zamani na kimiyya don farfado da wanda ya jigata.

Conrad ya samu isa cikin irin wannan managarcin asibitin a Jami’ar Pennsylbania, amma ba kai tsaye ya isa can ba. Jami’ai sun yi gaugawar kai shi wani karamin asibiti, amma ma’aikatan wurin sun kasa gano cutar da ke damun Conrad – don bai yi kama da masu fama da ciwon bugun zuciya ba, saboda haka ba su san abin da ya dace su yi a kansa ba, ta yadda zai rayu. Matar Conrad, wacce likita ce, daga bisani ta iso, kuma ta tuna cewa ta taba jin yadda aka yi wani bincike kan tasirin farfado da majiyaci ta hanyar samar da numfashi domin bugun zuciya ya dawo a wata jami’a dake kusa da asibitin da aka kai mijinta, sai ta jajirce kan a mayar da Conrad zuwa can.

Da yamma sai aka kwantar da shi a asibitin Jami’ar Pennsylbania, inda likita Benjamin Abella, shugaban bincike a cibiyar kimiyyar tasirin numfashi da bugun zuciya ya bayar da umarnin a sanyayya jikin Conrad don rage masa radadin zafin ciwo tare da tsagaita kai-kawon sinadarai wato al’amura biyu da ke taimaka wa jiki farfadowa daga raunin numfashi da bugun zuciya. Conrad ya some tsawon wasu kwanaki, inda a wadannan kwanakin aka yi masa maganin da ya hada da shawo kan hawan jini da wankin mara.

Ta yiwu da na kwanta a karamin asibiti da na murmure kuma na samu lafiya, kodayake ban sani ba,” in ji Conrad. “Sai dai na yi farin ciki ba ni ke kula da kaina ba.”

Matsaloli irin na Conrad ba baki ba ne. Kuma suna taimaka wa likitoci da masana kimiyya wadanda suka kware a dabarun kaimin numfashi da bugun zuciya.

“Ba lallai ba ne da zarar mutum ya mutu a ce kwakwalwarsa ta daina aiki ba, bata gama lalacewa ba tukun,” kamar yadda Sam Pamia ya bayyana, wanda shi ne babban shugaban cibiyar binciken kaimin numfashi da bugun zuciya a Jami’ar Stony Brook ta makarantar koyon aikin likita da ke birnin New York a Amurka. “Sai ka mutu, kwakwalwarka ma ta mutu, kafin a ce ka mutu gaba daya.”

A gaskiya, sabuwar fasaha da ilimi a lokacin kaimin numfashi da bugun zuciya, al’amarin na inganta fahimtarmu game da yanayin mutuwa. Masu bincike sun fara fahimtar cewa mutuwa na aukuwa ne a cikin wani lokaci sabanin a ce ta auku baki daya ne. Ko da zuciya ta daina bugawa, jiki zai kasance a raye na tsawon wasu sa’o’i – a wasu lokutan ma sukan yi kwanaki.

“A yanzu muna da bangarori biyu; gargarar mutuwa da mutuwa murus, saboda rashin kyakkyawar tarairaya,” inji Abella. “Ko rashin kai wa gargara. Tabbas lamari ne da aka kasa tantancewa tukuna.”

 

Mafi yawan mutane sun dauka mutuwa mai kwaf daya ce – mutum na raye, sai ya kasance babu shi. Ita ce mai kawar da rayuwa, da aka dauka cewa aukuwarta kawai da zarar zuciyar mutum ta daina bugawa. A yau, kimanin kashi 95 cikin 100 na katin shaidar mutuwa na amfani da wannan misalin a matsayin dalilin mutuwa, kuma dimbin mutane da suka rayu a tarihin dan Adam, wannan tunani ne da ke tabbatar da hakikanin gaskiya. Idan zuciyar mutum ta daina bugawa, sai a tabbatar da mutuwarsa ko mutuwarta. Sai a ce babu yadda za a farfado da su don su dawo su ci gaba da rayuwa.

A shekarun 1960, masu bincike sun kalubalanci irin wannan hasashen. Dannar kirji da hura iska daga baki-zuwa-baki na iya sauya rayuwar mutum zuciyarsa ta fara bugawa. Ko a wancan lokacin, likitoci sun dauka cewa da zarar jini ya daina gudana kwakwalwar mara lafiya za ta fara kifewa ko da an yi wa zuciya kaimi.

“Duk an koya mana cewa minti biyar ya rage mana da zarar zuciya ta daina bugawa,” inji Pamia. “Yanzu mun fahimci waccan tsohuwar fahimta ce, don a gaskiya kwayoyin halittar kwakwalwa ba sa mutuwa nan take.”

A cewar masu bincike kwayoyin halitta da kafofin jiki na da yanayin mutuwar su, wani tsari da ke daukar sa’o’i ko kwanaki ya danganta ga musababbin lamarin. Misali mafi tsanani, kwayoyin jijiyoyin halittar nama da ke jikin gawa na ci gaba da aiki har kwana 17, kamar yadda wani bincike ya gano a shekarar 2012, matukar ba gurbata su da iskar odygen ba.

Duk mutumin da bai farfado ba, bayan an yi masa kaimi na tsawon mintuna 20 zuwa 30, ta yiwu ba zai ta shi ba, amma wannan lokacin ba kayyade ba ne. “Ba mu san hakikanin lokacin da ake dauka bayan mutuwa da kwayoyin halitta za su rube su daina aiki, ta yadda ba za a iya motsa karsashinsu ba,” inji Pamia.

Mutane na daukar sa’o’i kafin su mutu murus. A wani muhimmin al’amari da ya faru a shekarar 2011, wata mata a kasar Japan, ta yi shirin halaka kanta, sai ta shiga daji, ta sha magani fiye da ka’ida. Washegari, wani mai wucewa ya ganta. Da masu kulawar gaugawa suka zo, yanayin zafin jikinta sentigirade 20 ne. Zuciyarta ba ta bugawa da numfashi.

Duk kokarin da aka yi na tayar da zuciyarta ya ci tura, amma maimakon a kaita wajen adana gawa, sai likitoci suka lika mata na’urar bijiro da iskar odygen a jijiya (ECMO), na’urar da ke aiki a matsayin huhu da zuciyar wucin gadi, bisa managarcin tsarin kular lafiya na kasar Japan, inda aka barta iskar ta ci gaba da kewaya jikinta.

Bayan sa’o’i ana gudanar da aikin, sai zuciyarta ta fara bugawa. Sanyin itatuwa ya hana kwayoyin halittar matar mutuwa cikin hanzari sabanin a ce a wuri mai zafi take, al’amarin da ya ba ta damar kwanciya a mace cikin daji na tsawon sa’a hudu, tare da farfadowar sa’a shida tsakanin lokacin da mai wucewa ya kira motar daukar marasa lafiya da lokacin da zuciyarta ta fara bugawa.

Bayan makonni uku aka sallameta daga asibiti, yanzu ta yi aurenta cikin farin ciki, har ta haifi jaririnta. “Da a ce daya daga cikin jami’an agajin gaugawa ne ya gano matashiyar da tuni an tabbatar da mutuwarta,” inji Pamia.

 

Tafiyar mamaci

Shawo kan mutuwa, tamkar kowace irin cuta, na bukatar fahimtar abokiyar gaba da yadda za a yaketa, kamar yadda Pamia ya bayyana a littafinsa “Kawar da mutuwa” (Erasing Death). Matakin farko, a yi wa zuciyar mara lafiya kaimi. Girgizar lantarki ta musamman za ta haifar da nasara ta hanyar sa’ido ga kaimin zuciya nan take. Fitar sauti da alamu da ke kara wa likitoci horon kwazon aiki, wadanda suka hada da umarnin ci gaba da aiki na tsawon lokacin kaimin da ake yi wa zuciya. Na’uarar na tattara bayanai don nazari.

Mafi yawan likitoci ba su damu da irin wadannan na’urorin ba. Kodayake an yi nuni da bukatar hakan. A daya daga binciken da aka gudanar, nasarar kaimin an kimanta ta da kashi 45 cikin 100, amma sanya likitoci amfani da sakamakon na’urar kaimin zuciya da lantarki na kara musu kimar nasararsu da kashi 60 cikin 100.

Sayen na’urorin kewaya iskar odygen a jiki (ECMO) irin na matar nan ‘yar Japan ba iya yi wa jiki kaimin aiki har likitoci su samu motsa zuciya ba. Na’urorin kan zuki jinin mara lafiya su kewaya da shi ya gauraye da cikakkiyar iskar odygen . A Koriya ta kudu da Japan, likitoci sun bayar da rahoton nasarar da kashi 90 cikin 100 wajen yi wa bugun zuciya kaimi da na’urar ECMO. A Amurka da Turai likitoci sun bayar da rahoton nasarar kashi 50 cikin 100 na kaimin zuciyar, sai dai babu wata dabarar da aka tsayu kanta da na’urorin ECMO.

A shekarar 2003, wasu asibitocin suka bullo da hanyar dumama jiki mafi sauki – irin wanda aka yi amfani da ita wajen kula da bugun zuciyar Conrad. Likitoci kan rage zafin jikin marasa lafiya da kimanin digiri hudu zuwa sentigrad 33, ta hanyar amfani da auduga ko siririn bututu don sanyaya jiki ta ciki. Wannan ke langabar da jiki a some, inda tsawon lokaci zai warware daga raunin farmakin zuciya. Kumburi da tursasawar kwakwalwa za su ragu da ayyukan kwayoyin halitta, wadanda suka hada da bai wa kwayoyin halitta umarnin halaka kansu. Daya daga binciken ya gano cewa kowane mara lafiya shida da aka yi musu irin wannan aiki daya ne ke warkewa.

Al’amuran na nuni cewa tattara bayanai da dabarun da ake amfani da su na fa’idantar da mu. A nazarin kimiyyar rayuwar halittu, idan har za ka iya yin hakan sau daya, tabbas za ka iya maimaitawa a karo na biyu,” a cewar Lance Becker, shugaban Cibiyar Kimiyyar Kaimin Numfashi da Bugun Zuciyara ta Pennsylbania. “Kuma idan ka warware matsalar, za ka iya yi a kowane lokaci.”

 

 

Exit mobile version