Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Shin Rashin Kokarin Barcelona Ne Zai Dawo?

by Abba Ibrahim Wada
February 13, 2021
in WASANNI
1 min read
Zaben Shugaban Barcelona
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ranar Talata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sha kashi a hannun Sebilla da ci 2-0 a gidan Sebilla a wasan daf da karshe zagayen farko a Copa del Rey kuma minti 25 da fara wasa Jules Kounde ya fara ci wa Sebilla kwallo, sannan tsohon dan wasan Barcelona, Iban Rakitic ya kara ta biyu daga baya.
Rabon Barcelona da kamfar cin kwallo tun karawar da Juventus ta doke ta ranar 8 ga watan Disamba a filin wasanta na Camp Nou a Champions League kuma tun daga lokacin tana cin kwallo a kalla daya ko fiye da haka a duk karawar da ta yi.
Tun bayan da Barcelona ta sha kashi a hannun Juventus ta yi wasanni 16, wadda kan zura kwallo a kowanne sannan cikin karawar da ta yi har da a gasar La Liga da Champions League da Copa del Rey da kuma Super copa de Espana.
Barcelona za ta karbi bakuncin wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey ranar 3 ga watan Maris har ila yau Barcelona wadda aka doke a wasan karshe a Spanish Super Cup za ta buga Champions League da Paris St Germain cikin watan nan na Fabrairu bugu da kari kungiyar wadda ba ta ci kofi ba a bara tana ta uku a kan teburin La Liga na bana.

SendShareTweetShare
Previous Post

Babu Wanda Zai Iya Dakatar Da Manchester City

Next Post

Shin Real Madrid Za Ta Iya Lashe Kofi A Wannan Kakar?

RelatedPosts

Ko Kun San Rayuwar Tiger Woods A Wasan Golf?

Ko Kun San Rayuwar Tiger Woods A Wasan Golf?

by Abba Ibrahim Wada
18 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Wada Dan wasa Tiger Woods dai na...

Ban Yi Da-na-sanin Barin Barcelona Ba – Suares

Ban Yi Da-na-sanin Barin Barcelona Ba – Suares

by Abba Ibrahim Wada
18 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Wada Tsohon dan wasan gaba na kungiyar...

Man City Ta Kama Hanyar Wasan Kusa Da Karshe A Kofin Zakarun Turai

Man City Ta Kama Hanyar Wasan Kusa Da Karshe A Kofin Zakarun Turai

by Abba Ibrahim Wada
18 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Wada Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa...

Next Post
real madrid

Shin Real Madrid Za Ta Iya Lashe Kofi A Wannan Kakar?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version