Abba Ibrahim Wada" />

Shin Za A Samu Sabon Messi Idan An Dawo Gasar Laliga?

Ranar Alhamis za a cigaba da gasar La Liga ta bana tun bayan da aka dakatar da wasanni a watan Maris, saboda tsoron yada cutar korona kuma a ranar Asabar Barcelona za ta yi wasan mako na 28, inda za ta ziyarci Real Mallorca.

Saboda haka Barcelona da Lionel Messi na shirin fuskantar kalubale da zarar an ci gaba da wasannin kakar shekarar nan saboda Barcelona na fatan lashe kofin La Liga na uku a jere da kuma kofin zakarun turai na Champions League, shi kuwa Messi na fatan samun nasarori na kashin kansa.

Kyaftin din na Barcelona shi ne na daya a cin kwallo a gasar La Liga da kwallaye 19 a raga da tazarar kwallaye biyar tsakaninsa da Karim Benzema wanda yake buga wasansa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Hakan na nufin Messi na shirin lashe kyautar wanda ke kan gaba a cin kwallo a La Liga kuma na bakwai jumulla wato kyautar “Pichichi” kamar yadda ake kiranta da harshen kasar Sipaniya sannan wannan bajintar zai sa Messi ya haura tsohon dan wasa Pedro Telmo Zarra wanda ya ci kyautar zama na daya a yawan cin kwallaye a La Liga mai guda shida.

Shi dai Telmo Zarra dan kasar Spaniya ya yi kusan rayuwar wasan kwallon kafarsa a kungiyar kwallon kafa ta Athletico Bilbao dake kasar ta Sipaniya daga shekarar 1940 zuwa 1955 inda ya ci kwallaye 335 a tarihi.

Sai dai dan wasan tawagar Brazil, Pele wanda ya ci kwallaye 643 shi ne ke kan gaba a tarihin wanda ya ciwa kungiya daya kwallaye da yawa a tarihi amma yanzu Messi yana da kwallaye 627 da ya ci wa Barcelona, kuma hakan na nufin saura kwallaye 17 dan kwallon na Argentina ya kafa nasa tarihin kuma ya kamo Pele.

Sauran wasanni  12 a karkare gasar La Liga da sauran wasanni nan gaba da Messi zai buga tunda da sauran kwarinsa har yanzu babu wanda ya san iya kwallayen da zai zazzaga a raga a tarihi kafin yayi ritaya.

Messi zai zama dan wasa na biyu da ya yi nasarar cin kofin Zakarun Turai na biyar kenan idan suka lashe na wannan shekarar, zai zama saura daya ya yi kan-kan-kan da Gento mai shida a tarihi a Real Madrid sannan zai kuma ci kofin La Liga na tara a shekara 12 kenan kuma na 11 daga 16 da aka fafata da shi aka ci kofin har ila yau Lionel Messi yaci kofuna 34 a Barcelona, idan ya ci La Liga da Champions League a bana zai yi kan-kan-kan da Ryan Giggs tsohon dan wasan Manchester United mai guda 34 a kungiya daya.

Exit mobile version