Kwanan baya, shugaban hukumar leken asiri ta kasar Birtaniya ko MI6 Richard Moore, ya gaya wa manema labarai cewa, a halin yanzu, kasar Sin ta riga ta kasance “babbar abar hukumarsa”, kuma hakan ya fi aikin yaki da ta’addanci muhimmanci a gare shi.
Ainihin yunkurinsa na zargin kasar Sin, shi ne shafa wa kasar bakin fenti kawai, wanda hakan ba shi da wani tushe ko kadan.
Hakika kasar Sin kasa ce da ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya mafi yawa zuwa yankunan da suke bukata, kuma sau da dama sojojin kasar sun samu lambar yabo ta MDD, amma duk da haka, cikin dogon lokaci, kasar Birtaniya ta ci gaba da haifar da hargitsi, da masifu a kasashe da yankuna da yawan gaske dake fadin duniya, tare da kasar Amurka kamar yadda suke so.
Ban da haka, Richard Moore, da takwaransa na Amurka, suna baza karairayi kan batun dake shafar yankin Taiwan na kasar Sin.
Ko shakka babu, ba zai yiwu su cimma yunkurinsu ba, Taiwan yankin kasar Sin ne, wanda ba za a iya raba shi daga kasar ba, ba kuma wanda zai iya hana dungulewar kasar Sin. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)