Gwamnonin jam’iyyar PDP za su gana da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, kan halin da ake ciki a Jihar Ribas, yayin da ake neman tsige gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara.
Darakta Janar na kungiyar gwamnonin PDP, CID Maduabum, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar bayan taron kungiyar a ranar Talata.
- Malaman Makaranta 1,700 Sun Koka Kan Rashin Biyan Su Albashin Shekaru 3Â
- CBN Ya Rufe Wasu Bankuna 754 Sakamakon Shiga Matsaloli
Gwamnonin za su gana da ministan a yau Laraba a ofishinsa.
Shugaban kungiyar, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ne zai jagoranci wasu gwamnoni kusan 10 na jam’iyyar PDP zuwa ofishin ministan babban birnin tarayya Abuja domin tattaunawa.
“Bayan shawarar da aka cimma a taron kungiyar gwamnonin PDP a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, za mu ziyarci Ministan babban birnin tarayya Abuja, domin sasanci,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta yi taro ne a ranar Talata inda ta bukaci ‘yan siyasa a Kudu-maso-Kudu da su yi wani abu don warware rikicin cikin ruwan sanyi.
Wadanda suka halarci taron sun hada da: Gwamna Bala Mohammed (Bauchi), Gwamna Ahmadu Fintiri (Adamawa), Gwamna Sheriff Oborevwori (Delta), Gwamna Ademola Adeleke (Osun), Gwamna Seyi Makinde (Oyo), Gwamna Caleb Mutfwang (Filato), Gwamna Godwin Obaseki. (Edo), Gwamna Kefas Agbu (Taraba), Gwamna Dauda Lawal (Zamfara), Gwamna Siminalayi Fubara (Ribas) da Mataimakin Gwamna Ifeanyi Ossai (Enugu).
A wajen taron, gwamnonin PDP sun yi maraba da shiga tsakani da shugaba Bola Tinubu ya yi ta hanyar ganawa da Fubara da Wike a fadar Aso Villa da ke Abuja da yammacin ranar Talata domin warware rikicin.
Ganawar da shugaban kasar ya yi da ‘yan siyasar biyu na PDP ya biyo bayan yunkurin tsige Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas ta yi a ranar Litinin.
Majalisar dokokin jihar ta zargi gwamnan da aikata munanan ayyukan da ba su dace ba a matsayinsa na gwamna.