Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Wasan Najeriya Mahalarta Gasar Olympic Ta Beijing 2022 Fatan Nasara Gami Da Taya Sin Murna

by
4 months ago
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Wasan Najeriya Mahalarta Gasar Olympic Ta Beijing 2022 Fatan Nasara Gami Da Taya Sin Murna
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga CRI Hausa,

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, a madadin dukkan ’yan Najeriya, yana yiwa ’yan wasan Najeriyar mahalarta gasar wasannin Olympic ta Beijing 2022 ta lokacin hunturu da ta ajin nasakassu na gasar fatan samun nasarori.

A cewar shugaban, ya yi amanna cewa, ’yan wasan Najeriyar da za su fafata a wasanni daban daban a lokacin gasar za su taka rawar gani, inda ya yaba musu bisa nasarorin da suka samu a gasar wasannin da suka halarta a PyeongChang na kasar Koriya ta kudu a shekarar 2018, inda kasar ta shiga gasar a karon farko.

Labarai Masu Nasaba

Wang Wenbin: Fatanmu Shi Ne Amurka Ta Aiwatar Da Abubuwan Da Ta Alkawarta

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Kara Hada Hannu Wajen Daidaita Kasuwar Abinci Ta

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa, wasannin Olympic wani dandali ne na karfafa abokantaka da hadin kai tsakanin kasashen duniya. Yana fatan dukkan wasannin, za su cimma burikan da ake fatan cimmawa a Olympic wajen daga matsayin ruhin wasanni, da karfafa zumunci, da kuma mutunta juna.

Shugaban Najeriyar ya taya kasar Sin murnar karbar bakuncin gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu, inda ya yabawa gwamnatin Beijing bisa tarihin da birnin ya kafa inda ya kasance birnin da ya karbi bakuncin gasar wasannin Olympic har karo biyu a tarihin wasannin, kasancewar birnin ya taba karbar bakuncin gasar wasannin Olympic na lokacin zafi a shekarar 2008.

A matsayinta na aminiya kuma ’yar uwa ga kasar Najeriya, shugaba Buhari ya bada tabbacin goyon bayan gwamnati da al’ummar Najeriya ga kasar Sin.

Sannan ya yi amanna cewa, bisa irin dunbun kwarewar da kasar Sin ta samu wajen tsara manyan tarukan kasa da kasa, gasar wasannin Olympic ta Beijing 2022, mai taken “Hadin gwiwa tare don samar da makomar bai daya”, za a gudanar da gasar cikin nasara kamar yadda aka tsara, kuma gasar za ta baiwa duniya mamaki tare da karya matsayin bajinta a tarihin wasannin Olympic na kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Hauhawar Farashi A Amurka Zai Iya Illata Duk Duniya

Next Post

Mataimakin Shugaban IOC Ya Ce Gasar Olympics Tamkar Gada Ce Ba Katanga Ba

Labarai Masu Nasaba

Wang Wenbin: Fatanmu Shi Ne Amurka Ta Aiwatar Da Abubuwan Da Ta Alkawarta

Wang Wenbin: Fatanmu Shi Ne Amurka Ta Aiwatar Da Abubuwan Da Ta Alkawarta

by CMG Hausa
11 hours ago
0

...

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Kara Hada Hannu Wajen Daidaita Kasuwar Abinci Ta Duniya

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Kara Hada Hannu Wajen Daidaita Kasuwar Abinci Ta

by CMG Hausa
11 hours ago
0

...

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Kara Hada Hannu Wajen Daidaita Kasuwar Abinci Ta Duniya

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Kara Hada Hannu Wajen Daidaita Kasuwar Abinci Ta Duniya

by CMG Hausa
11 hours ago
0

...

MOC: Dalilan Da Ke Jawo Jarin Waje A Kasar Sin Ba Su Canja Ba

MOC: Dalilan Da Ke Jawo Jarin Waje A Kasar Sin Ba Su Canja Ba

by CMG Hausa
14 hours ago
0

...

Next Post
Mataimakin Shugaban IOC Ya Ce Gasar Olympics Tamkar Gada Ce Ba Katanga Ba

Mataimakin Shugaban IOC Ya Ce Gasar Olympics Tamkar Gada Ce Ba Katanga Ba

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: