Shugaba Bola Tinubu ya amince da sake gina babbar gadar Wagga da ta haɗa jihohin Adamawa da Borno, bayan rushewar ta karo na biyu cikin watanni biyu. Mohammed Goni, Darakta Janar na hukumar cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC), ya sanar da wannan yayin duba wurin da lamarin ya faru a ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
Gadar, wadda take da matuƙar muhimmanci wajen sauƙaƙe tafiye-tafiye tsakanin jihohin biyun, ta lalace ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
- Mutum 68 Sun Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Sudan
- PDP Ta Jajantawa Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kebbi
Goni ya bayyana cewa bayan binciken farko, an shirya fara gyaran gadar, amma rushewar da ta sake yi ne ya sa aka yanke shawarar sake gina ta gaba ɗaya. Ya shaida cewa daminar bana na iya jinkirta fara aikin, amma za a ɗauki matakan wucin gadi don ba da damar zirga-zirgar motoci.
Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa amincewar da Shugaba Tinubu ya yi za ta kawo sauƙi kuma ta rage wahalhalun da mutane ke fuskanta yayin tafiya tsakanin Adamawa da Borno.