Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da rusashshiyar kungiyar gwamnonin G-5 a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.
G-5 dai ta kunshi gwamnonin PDP biyar – Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Samuel Ortom (Benue), Seyi Makinde (Oyo) da Nyesom Wike (Ribas).
A cikin gwamnonin G-5, Gwamna Makinde ne kadai ke rike da mukamin gwamna a yanzu.
Fusatattun Gwamnonin dai sun kulla kawance ne bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ya lashe a watan Mayun 2022.
Sun bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa na lokacin, Iyorchia Ayu, ya sauka daga mukaminsa, wannan shine sharadin da gwamnonin suka bayar na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu amma hakan bata samu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp