Gwamnmatin tarayya ta hannun ma’aikatar bunkasa harkokin ma’adanai ta yi alkawarin aiki tare da manya-manyan kamfanonin harkokin ma’adanai na duniya don fitar da tsari na musamman da zai kai Nijeriya ga cin cikakkiyar gajiyar ma’adanai daban-daban da Allah ya shimfida a sassan kasar nan, wannan kuma zai zo ne a karkashin matakai 7 da gwamnati Shugaban kasa Bola Amed Tinubuy ya tsara.
Sanarwar haka ta fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga Ministan harkokin ma’adanai, Segun Tomori, ya kuma ce, wannan hadin gwiwar zai bunkasa sashin ta yadda zai kai ga samar wa Nijeriya kudin shiga mafi girma a cikin bangarorin tattalin arzikin kasar nan.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-17 Dauke Da ’Yan Sama Jannati
- Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe
Da yake karbar bakuncin shugaban kamfanin ma’adanai na ‘PWC Partner’, Habeeb Jaiyeola, a ofishinsa, Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya yaba wa gudummawar kamfanin a nasarar da aka samu wajen gudanar da bikin makon ma’adanai da aka yi kwanakin baya.
Ya kuma gode wa shugabanin kamfanin a kan yadda ya jagoranci bangaren hakar ma’adanai a Nijeriya na tsawon shekaru, ya kuma yi alkwarin jawo su a jiki wajen kokarin samarwa da bangaren hakar ma’adanai alkibla na gari karkashin matakai 7 da Shugaba Bola Tinubu ya tsara. Ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana neman mayar da bangaren hakar ma’adanai kan gaba wajen samar wa Nijeriya kudin shiga.