Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai tafi Brazil domin halartar taron shugabannin ƙasashen G20 karo na 19, wanda zai gudana daga ranar Litinin, 18 ga Nuwamba, zuwa Talata, 19 ga Nuwamba.
Taron na bana, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, yana da taken “Gina Duniya Mai Adalci da Ɗorewar Muhalli.” Za a tattauna batutuwa kamar yaƙi da yunwa da talauci, gyaran dokokin hukumomin duniya, da ci gaba mai dorewa, da sauyin makamashi.
- Asirin Barawon Da Ake Zargin Ya Sace Kudin Da Ake Tarawa A Coci Ya Tonu
- Ko Shakka Babu Tinubu Ne Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa A 2027 – APC
Wannan tafiya na zuwa ne kwana biyar bayan dawowar Tinubu daga Saudiya, inda ya halarci taron koli na haɗin gwuiwar ƙasashen Larabawa da Musulmi, wanda Sarki Salman da Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman, suka shirya. Tafiya Brazil ta biyo bayan gayyatar Shugaban Brazil kuma shugaban G20 na yanzu, Luiz Inacio Lula da Silva, inda Shugaba Tinubu zai yi muhimmiyar ganawa kan batutuwan duniya.
Tinubu zai yi amfani da wannan damar wajen gudanar da taruka na bangarorin biyu domin karfafa tsarin gyare-gyaren tattalin arziƙin da zamantakewar Nijeriya. Ya kasance tare da manyan jami’an gwamnati kamar Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar da Ministan ci gaban kiwo, Idi Mukhtar Maiha da Ministan buɗe idanun da Al’adu, Hannatu Musawa da shugaban hukumar leken Asiri ga ƙasa Mohammed Mohammed.