Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce ya yi imani duk yadda aka samu sauye sauye a harkokin kasa da kasa, kasarsa da Hungary za su ci gaba da kallon alakar su daga mahanga mai fadi a kuma tsawon lokaci.
Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a ranar Laraba, cikin rubutaccen jawabin da ya gabatar yayin da ya sauka a kasar Hungary, inda ya fara gudanar da ziyarar aiki.
- Sin Na Adawa Da Kalaman Amurka Na Karfafa Kasancewar Taiwan A Taron WHO
- An Gudanar Da Bikin Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Serbia A Belgrade
Har ila yau, shugaban na Sin ya ce kasarsa da Hungary kawaye ne na hakika, kuma abokai na gari da suka amince da juna. Ya ce a bana ake cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, wanda hakan ya kawo muhimmiyar dama ta bunkasa alakar su.
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce yana fatan ganawa da shugaba Tamas Sulyok, da firaminista Viktor Orban da sauran wasu jagororin kasar ta Hungary, tare da hada kai da su wajen shata sabon tsarin hadin gwiwa da samar da ci gaba, da nufin dora alakar kasashen biyu kan turbar babban ci gaba, da daga matsayin ta zuwa mataki na gaba.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa birnin Budapest fadar mulkin kasar Hungary a ranar Laraba 8 ga watan nan na Mayu bisa agogon wurin, bisa gayyatar da shugaban kasar Hungary Tamas Sulyok da firaministan kasar Viktor Orban suka yi masa, don yin ziyarar aiki a kasar ta Hungary.(Saminu Alhassan)