A yau Juma’a 30 ga watan Disamba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin maraba da sabuwar shekarar 2023, ga taron ‘yan majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC.
Cikin jawabin na sa, shugaba Xi ya ce shekarar 2022 ta kasance mai matukar muhimmanci a tarihin JKS da kasar Sin.
Domin kuwa a shekarar ne aka gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara, inda kuma aka zayyana tsarin gina kasar Sin zuwa kasar gurguzu ta zamani daga dukkanin fannoni. Shugaban na Sin ya kara da cewa, Sin ta ci gaba da bunkasa ta fuskar tattalin arziki, ta kuma samu yabanya mai yalwa, tare da tabbatar da daidaito a fannin samar da guraben ayyukan yi, da farashin kayayyaki a shekarar ta 2022.
Kaza lika shugaba Xi ya ce Sin ta inganta matakan ta na shawo kan annobar COVID-19 daidai da yanayin da take ciki, domin tabbatar da kare al’umma da rayukan su gwargwadon ikon ta, kuma bisa yanayi mafi kankantar haifar da tasiri kan tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al’ummar ta.
Xi ya ce a shekarar 2022, majalissar CPPCC ta aiwatar da shawarwari, da tsare-tsaren kwamitin tsakiya na JKS, ta kuma bayar da sabbin gudummawa wajen gudanar da ayyukan JKS da ma kasar Sin baki daya.
Daga nan sai shugaba Xi ya bayyana fatan cewa, a shekarar 2023 da za a shiga, majalissar ta CPPCC za ta kara azama, wajen tabbatar da kara dunkulewar jagorancin JKS, ta yadda jam’iyyar za ta wanzar da ikon ta na zama jigo, kuma dandali na tabbatar da dimokaradiyya, wanda hakan zai ba da damar cin gajiya daga basira da karfin ikon ta, har a kai ga cimma nasarori, da ayyukan da aka sanya gaba, a sabuwar tafiyar wannan sabon zamani. (Saminu Alhassan)