Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai ziyarci yankin musamman na Macao na kasar Sin, tsakanin ranakun 18 zuwa 20 ga watan nan na Disamba, don halartar bikin cikar yankin Macao shekaru 25 da komowa kasar Sin.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojin kasar Sin, zai kuma halarci bikin kaddamar da gwamnatin yankin na Macao ta 6. Kaza lika, zai yi rangadin aiki a yankin na Macao. (Saminu Alhassan)