A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da kantoman yankin musamman na Macao Sam Hou Fai, wanda ke ziyarar aiki a birnin Beijing.
A lokacin tattaunawar, Xi ya saurari rahoto dangane da halin da yankin Macao ke ciki, da aikin gwamnatin yankin daga Sam Hou Fai.
Shugaba Xi ya ce gwamnatin tsakiya ta gamsu matuka da aikin Sam da gwamnatin yankin musamman na Macao. Ya kuma yi kira ga gwamnatin yankin musamman na Macao da ta yi aiki tukuru wajen daidaita tafiya da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, da goyon baya da inganta jagorancin gwamnati, da dagewa wajen ingiza matakai wadanda za su fadada bunkasar tattalin arzikin Macao, da kyautata hade yankin cikin tsarin da zai samar da gudummawar raya ci gaban kasa baki daya. (Saminu Alhassan)














