• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Najeriya

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Xi

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Najeriya Bola Tinubu a yau Talata, yayin da shugaba Tinubu ya iso birnin Beijing domin halartar taron FOCAC na 2024, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin.

Yayin zantawarsu, shugaba Xi Jinping ya ce Najeriya muhimmiyar kasa ce mai tasirin gaske a nahiyar Afirka, kuma kasa mai yawan al’umma da damar samun bunkasuwa. Ya ce a matsayin su na manyan kasashe masu tasowa, Sin da Najeriya za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa bisa matsayin koli, wanda hakan zai sanya sabon kuzari ga dangantakar sassan biyu a sabon zamani, tare da jagorantar kasashen dake samu saurin ci gaba, da masu tasowa wajen gudanar da ayyuka tare.

  • Nijeriya Ta Jaddada Ƙudirin Ƙarfafa Ƙawance Da Indonesiya
  • Matatar Man Dangote Ta Fara Sarrafa Man Fetur

A nasa bangare, shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya ce, kasarsa tana son zama abokiyar kasar Sin mafi girma a fannin hadin gwiwar cinikayya da zuba jari a nahiyar Afirka. Kana ana son ganin karin kamfanonin kasar Sin su zuba jari da karfafa huldar hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da masana’antu, da makamashi, da dai sauransu a kasar Najeriya.

LABARAI MASU NASABA

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin huldar kasashensu zuwa abokantaka da ta shafi manyan tsare-tsare na dukkan fannoni. Bayan ganawar su, sun kuma ganewa idanun su bikin sanya hannu kan takardun bunkasa hadin gwiwar kasashen su.

Har ila yau a dai Talatar nan, shugaba Xi ya gana da shugabannin kasashen Mauritania, da Zimbabwe da karin wasu kasashen. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
Daga Birnin Sin

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
Next Post
An Gudanar Da Taron Ministoci Na Dandalin FOCAC Karo Na 9 A Beijing

An Gudanar Da Taron Ministoci Na Dandalin FOCAC Karo Na 9 A Beijing

LABARAI MASU NASABA

Abduljabbar

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025
Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
peter

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.