Shugaban kasar Equatorial Guinean Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya ce tun kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar sa da Sin, sassan biyu ke ta goyon baya da taimakawa juna, wanda hakan ya haifar da gagarumin sakamako, da bunkasar ci gaba da walwalar su.
Shugaba Obiang, wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan, ya ce “Sin ta goyawa Equatorial Guinea baya a fannoni da dama, da suka hada da tattalin arziki da na fasahohi. Kuma Equatorial Guinea ta gamsu da tallafi da take samu daga jamhuriyar al’ummar kasar Sin. Ana iya cewa wani bangare na irin managarcin sauyi da Equatorial Guinea ta samu, yana da alaka kai tsaye da tallafin raya tattalin arziki da gwamnatin kasar ta samarwa kasar.
Ana sa ran bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaba Obiang, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin tun daga gobe Lahadi 26 ga watan nan na Mayu zuwa 31 ga wata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)