Khalid Idris Doya" />

Shugaban Faransa Ya Bukaci Kamfanonin Kasarsa Su Zuba Jari A Rasha

Shugaba Emmanuel Macron, na Faransa ya yi kira ga kamfanonin kasarsa akan su kara zuba jari a Rasha, musamman a bangaren da suka fio karfi kamar abincin na safarawa da harkokin sarararin samaniya da kuma kayan lataroni.

Mista Macron ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da yake a Rasha a inda kuma yake halartar babban taron kasuwanci na haddn gwiwar kasashen Rasha da Faransa, a birnin Saint-Petersbourg.

A nasa bangare shugaba Putin ya shaida cewa, Faransa babbar abokiyar huldar Rasha ce, inda ya yaba da habakar cinikayar dake tsakanin kasashen biyu, wanda ya kai 16,5% a 2017, duk da a cewarsa yana kasa da harkokin kasuwancio da China, abokiyar huldar kasar Rashar ta farko.

Faransa dai nada kamfanoni da yawansu ya kai 500 a kasar Rasha wanda ke aiki a fanonin da suka hada da makamashi, masana’antu da harkokin kudi.

Daga cikin yarjejeniyoyi hamsin da kasashen biyu suka sanya wa hannu a yayin ziyarar ta Macron a Rasha, har da ta kamfanin Total wanda zai zuba jari na Dalar Amurka Bilyan 2,5 a harkar iskar Gaz.

Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Ce Takunkuman Amurka Ga Hizbullah Ba Zai Taba Yin Tasiri Ba

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa takunkuman da gwamnatin Amurka ta dorawa kungiyar ba za su yi wani tasiri a kan harkokin kungiyar ko kuma wadanda aka ambata a takunkumin ba.

Tashar talabijin ta Presstb ta nakalto Sayyid Nasrallah yana fadar haka ne a yammacin shekaran jiya Jumma’a a wani jawabin kai tsaye ta allunan talabijin da ya yi wa masu goyon bayan kungiyar.

Sayyid Nasarallah ya kara da cewa manufar gwamnatin Amurka da wadannan takunkuman ita ce nisanta mutanen kasar daga kungiyar, musamman ganin yadda suka fito konsu da kwarkwatansu suka zabi wakilan kungiyar a zaben majalisar dokokin kasar wanda aka gudanar a ranar 6 ga watan da muke ciki.

Duk da haka Sayyid Hassan Nasarallah ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin kasar Lebanon ta fitar da wani tsari wanda zai kare wasu na kusa da kungiyar wadanda mai yuwa takunkuman Amurka zata shafa.

A wani bangaren na jawabinsa shugaban kungiyar ta Hizbillah mai gwagwarmaya da HKI da kuma ‘yan ta’adda a ciki da wajen kasar Lebanon ya ce, kungiyarsa ba ta ‘yan ta’adda ba ce kamar yadda gwamnatin kasar Amurka take son ta nunawa duniya.

Ya ce kungiyarsa tana kare kasarta da kuma mutanen yankin ne daga HKI da kuma ‘yan ta’addan kuma tana da ‘yancin yin haka duk da cewa hakan zai shafi maslahar Amurka da kawayenta a yankin.

Daga karshe Sayyid Hassan Nasarallah ya kammala da cewa zaben ranar 6n ga watan Mayu da muke ciki ya nuna irin yadda mutanen kasar ta Lebanon suke kaunar kungiyar Hizbullah.

Don hake ne ma gwamnatin Amurka take son azabtar da su wanda ya ce haka din ba zai yi wani tasiri ba.

 

 

Exit mobile version