Shugaban karamar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi, Alhaji Zayyanu Muhammad Bello ya rasu.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Kebbi, Alhaji Ahmed Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
- Oluremi Tinubu Ta Tallafa Wa Tsofaffi 250 Da N100,000 Kowannensu A Kebbi
- ‘Yansanda Sun Kashe Wasu Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane 6, Sun Kwato Kudade A Bauchi
Ya ce, Zayyanu ya rasu yana da shekaru 47.
Ya ce shugaban ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
“Gwamnatin jihar Kebbi na son yin amfani da wannan kafar domin mika ta’aziyya ga iyalansa da daukacin al’ummar karamar hukumar Maiyama.
“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa dukkan kurakurensa, Ya kuma sa Jannatul Firdaus ce makomarsa,” inji shi.
A cewar hadimin gwamnan, marigayin, ya bar mata biyu da ‘ya’ya uku.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp