Kwanan baya, yayin taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawar Sin da CELAC, shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya ziyarci kasar Sin, inda kuma ya zanta da kafar CMG a shirin “Hira da shugabanni”.
Yayin tattaunawar, shugaba Petro ya ce ya sha ziyartar kasar Sin cikin shekaru 20 da suka gabata. Ya kuma yi imanin cewa, ayyukan kasar Sin sun nuna wani sabon salo na ci gaban zamantakewar al’ummar bil’adama. Ya ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara a fannin raya tattalin arziki da kawar da talauci, daruruwan miliyoyin mutane sun tsira daga kangin talauci, kuma sha’anin kawar da talauci a duniya ya samu gagarumin ci gaba. Shugaba Petro ya kara da cewa, wadannan nasarori ba a iya raba su da gudunmawar da Sin ta bayar.
Shugaban ya kuma ce, a duniyar yau mai gaggawar samun ci gaba a fannin kimiyya da fasaha, kasar Sin ta samu mukaminta, wato ta kai ga iya hada fasahar AI, da tattalin arzikin dijital da makamashi mai tsabta da sauransu, wanda hakan zai zama jigon tattalin arzikin duniya a nan gaba, ta yadda za a iya shiga wani sabon salo zamantakewa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp