Da yammacin jiya Litinin, babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS Xi Jinping, ya ziyarci kauyen Zhaoxing na kabilar Dong dake gundumar Liping na yankin Qiandongnan na kabilun Miao da Dong mai cin gashin kansa na lardin Guizhou, don gano kokarin da ake yi na karfafa kafa sassan JKS a kauyuka da mulkin zamantakewar al’umma, da kare da gadon al’adun gargajiya na kabilu, da sa kaimi ga farfado da yankunan karkara a dukkan fannoni da dai sauransu.
Yayin ziyarar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata cewa, ya kamata lardin ya aiwatar da matakan raya yankin yammacin kasar da raya tattalin arzikin yankin kogin Yangtze da kwamitin koli na Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya tsara, tare da nacewa ga samun ci gaba mai inganci ta hanyar zurfafa gyare-gyare da bude kofa.
- Trump Zai Tattauna Da Putin Kan Kawo Ƙarshen Yaƙin Ukraine
- Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Kwamishinan Ganduje Kan Zargin Ɓatan N240m
Shugaba Xi ya bayyana cewa, ci gaba mai inganci abu ne da ya zama wajibi a tafarkin zamanantar da kasar Sin. Ya kara da cewa, ya dace lardin Guizhou ya nacewa ga raya tubalin tattalin arziki mai nasaba da samar da kayayyaki da hidimomi, da karfafa ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire da gaggauta daukakawa da yi wa masana’antu garambawul da inganta tattalin arzikin dijital da makamashi mai tsafta.
An gina kauyen Zhaoxing na kabilar Dong a shekarar 986, wanda yana daya daga cikin kauyukan kabilar Dong mafi girma a kasar, kuma an bayyana shi a matsayin daya daga cikin tsoffin kauyuka na kasar Sin, kana sanannen kauye ne dake da dogon tarihi da al’adu na kasar Sin.
A cikin ’yan shekarun baya, kauyen Zhaoxing na kabilar Dong ya kara samun karfin ba da kariya ga tsoffin gine-gine da tsarin gidaje a cikinsa, ya kuma mayar da bukukuwan al’adun kabilu zuwa kayayyakin yawon bude ido, lamarin da ya sa mazauna kauyen sama da 2000 suka samu ayyukan yi da kuma harkokin kasuwanci. (Safiyah Ma, Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp