Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa takwaransa na Saliyo wasikar taya murnar sake lashe zaben shugabancin kasar sa, wadda a cikin ta ya bayyana cewa, Sin da Saliyo suna da dogon tarihi na sada zumunta da juna, kuma a shekarun baya bayan nan kasashen biyu na ci gaba da inganta amincewa da juna ta fuskar siyasa, sun kuma cimma manyan sakamako a fannonin hadin gwiwa na zahiri, tare da aiki tare a fannonin harkokin kasa da kasa.
Kaza lika shugaba Xi ya ce yana dora muhimmancin gaske, ga bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Saliyo, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Bio, a fannin goyon bayan juna, da aiki kafada da kafada wajen ingiza ci gaban dangantakar abokantaka, ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Saliyo, domin cin gajiyar al’ummun su. (Saminu Alhassan)