A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da masu fasaha daga kamfanin wasannin fasaha na Oriental na kasar Sin suka rubuta masa, inda ya yi nuni da cewa, a cikin wadannan shekarun da suka gabata, masu fasahar sun gabatar da shirye-shirye da dama masu kyau, wadanda suka samar da muhimmiyar gudummawa kan raya adabi da fasaha, da yin musayar al’adu da kasashen waje, sun kasance wakilan kasar Sin ta fuskar al’adu. Shugaba Xi yana fatan za su ci gaba da samar da sabuwar gudummawa wajen raya kasa mai tsarin gurguzu a fannin al’adu.
Yau shekaru 70 da suka gabata ne, an kafa kamfanin wasannin raye-raye na kasar Sin, sannan yau shekaru 60 da suka gabata, an kafa kamfanin nune-nunen wakoki da raye-raye na Oriental na kasar Sin. Yau wasu shekarun da suka gabata ne, an hada su an kafa kamfanin wasannin fasaha na Oriental na kasar Sin. (Zainab Zhang)