Connect with us

Uncategorized

Shugaban Kongo Ya Bukaci Bai Wa Tsaffin Shugabanni Kariya

Published

on

Majalisar Jamhuriyar Congo za ta yi zama na musamman akan kudurin da shugaban kasar Joseph Kabila ya mika mata, na samar da wata doka, da za ta bai wa shuwagabannin kasar kariya daga dukkan wata tuhumar aikata ba dai dai ba, bayan sauka daga mulki.
To sai dai har yanzu majalisar kasar ba ta yi karin bayani akan rana ko lokacin da za ta zauna domin muhawara akan wanna kuduri ba.
A karkashin dokar dai ba za a kama tsohon shugaba da mataimakansa ba, a dalilin aikata ba dai ba, zalika za a bai wa tsohon shugaban masu tsaron lafiyarsa na musamman, a kuma kara masa yawan kudaden fanshon da zai rika karba.
Wasu na kallon bukatar ta Kabila a matsayin alamar da ke nuni da cewa, shugaban ba zai sake neman tazarce ba, a zaben shugabancin kasar da zai gudana a watan Disamba mai zuwa, duk da cewa ‘yan adawa na zarginsa da shirya makarkashiyar kara wa’adinsa da ke gaf da karewa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: