Babban limamin jihar Legas Sheikh Garuba Ibrahim Akinola ya rasu a yammacin jiya Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya a asibitin jihar.
Sheikh Garuba Ibrahim Akinola ya rasu ya na da shekaru 79.
An dai zabi Sheikh Garuba Ibrahim Akinola a matsayin shugaban limaman jihar Legas a shekarar 2000, a yau litinin ne za a yi jana’izarsa .
Gwamnan jihar Lagos Akinwunmi Ambode, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan limamin.