Shugaban majalisar dandalin Asiya na Boao Ban Ki-moon ya ce, a cikin duniya mai dorewa, bai kamata a samu wani mai fama da talauci ba, ko mutuwa sakamakon cututtukan da ake iya magance su ba. Don haka, tilas ne kasa da kasa su yi hadin gwiwa tare da goyon bayan juna idan akwai bukata.
Ban Ki-moon ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin CMG a baya-bayan nan.
A wannan fanni, kasar Sin ta riga ta sa kaimi ga nuna goyon baya ga juna a duniya ta hanyar shawara “ziri daya da hanya daya”. Ban da wannan kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da kiraye-kiraye 3 ga duniya, wato kiran tabbatar da tsaron duniya, da kiran samun bunkasuwar duniya, da kuma kiran raya wayewar kan duniya. Ban Ki-moon ya yabawa wadannan kiraye-kiraye uku da shugaba Xi Jinping ya gabatar bisa hangen nesa. Yana fatan za a taimakawa kasashe masu tasowa da suke bukata wajen taka hanyar samun bunkasuwa mai dorewa a nan gaba. (Zainab)