Daga Muhammad Maitela,
Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana alhininsa tare da ta’aziyyar rasuwar wakilin gidan rediyon muryar Amurka (BOA), wanda ya rasu biyo bayan hatsarin motar da ya rutsa dashi.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ta hanyar ofishin sa mai hulda da kafafen yada labarai ya fitar ranar Asabar, a birnin Abuja.
A sakon ta’aziyar, Dr Ahmad Lawan ya bayyana cewa ya kadu sosai a lokacin da ya samu labarin rasuwan wakilin muryar Amurka a jihohin Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz, a ranar Juma’a.
Bugu da kari kuma, Dr Ahmad Lawan ya bayyana marigayin a matsayin abun koyi ga na baya, musamman matasa. Yace muryar Amurka dama sauran kafofin yada labarai sun yi rashin hazikin gwarzo a aikin radiyo na kasa da kasa.
A karshe shugaban majalisar dattawan ya mika ta’aziyya ga yan uwa da iyalan marigayin tare da addu’ar samun gafara da bai wa yan uwan hakurin jure wannan babban rashi da fatan Aljanna ta kasance makomarsa.