Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya taya shugaban kasa, Muhammadu Buhari murnar zagayowar cikar sa shekaru 78 da haihuwa, wanda ya yi daidai da ranar Alhamis da ta gabata.
Sanata Lawan, ya bayyana hakan a takardar sanarwar manema labarai wadda ofishin sa ta fitar kana kuma wadda ya rattaba wa hannu a ranar Laraba inda ya bayyana ranar a matsayin mai muhimmanci ga yan Nijeriya baki daya.
”Ina mai farincikin haduwa da yan uwa da iyala, abokai, jami’an gwamnati, na huldar yau da kullum da shugaban kasa wajen taya shi murnar wannan muhimiyyar rana wadda yake bikin tunawa da cikar sa a wannan matsayi na shekaru a cikin koshin lafiya da karsashi.”
”A duk shekarun da shugaba Buhari ya yi, bai gushe ba ya na gudanar da shugabancin kasar nan cike da nuna cikakkiyar jajircewar sa wajen ganin ya samar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban Nijeriya tare da samarwa yan kasa walwala.” In ji shi.
”Saboda haka ina kira ga dukkan yan kasa su fadada tunanin su da hangen nesa, kana su ci gaba da tsayawa kafaza da kafada tare da bayar da cikakken goyon baya ga manufofin gwamnatin shugaban kasa a wannan aiki da yake yi wajen sanya kshin kasa a zukatan yan Nijeriya.”
”Kuma a matsayi na na dan jama’iyar APC, ina mai farin ciki da yadda shugaba Buhari ya damra aniyar gyare-gyare da sake gina wannan kasaitarciyar jama’iyar tamu don ganin ta cimma burinta na shugabantar Nijeriya a cikin kyakkywan yanayi tare da ci gaban mulkin dimukuradiyyk da tattalin arziki.”
”Sannan a bangaren mu na yan majalisar dokoki na tarayya za mj ci gaba da aiki cikin tsanaki da kwanciyar hankali tsakanin mu da bangaren zartswa domin samun dawamamen zaman lafiya da ci gaban Nijeriya da al’ummarta baki daya.”
A karshe ya ce, a wannan rana mai muhimmanci ta zagoyowar ranar da aka haifi shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a ciki ya ke addu’a ga Allah madaukakin sarki ya ci gaba da bai shugaba Buhari fasaha, karfin gwiwa da lafiya don samun ci gaba da jagorantar Nijeriya a matsayin da yan kasa ke muradi.