Kungiyar Fulani Matasa ta Nijeriya (FUYAN) ta yi tir da ci gaba da tsare Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo yanzu kusan fiye da kwanaki 14 kenan ba tare da sanin halin da yake ciki ba.
Alhaji Bodejo, mutum ne da ya tsayu wajen fatan alhairi ga kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da kuma Nijeriya gaba daya.
- Fintiri Ya Dakatar Da Jigilar Kayan Aikin Gini Daga Adamawa Zuwa Kasashe Makwabta
- Abuja Na Fuskantar Baranazar Tsaro -Majalisar Dattawa
kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasaa da Bodejo ke shugabanta, kungiya ce da ta tsayu wajen tabbatar da kare al’adu da muradun al’umma Fulani a fadin tarayyar Nijerya. kungiya ce da aka yi wa rajista da hukumar yi wa kungiyoyi da kamfanoni rajista a Nijeriya (CAC) tana kuma bin dukkan dokoki da ka’idojin da hukuma ta sanya na tafiyar da kungiyoyi irinta a Nijeriya.
An samu nasarar kafa kungiyar ne bayan kiraye-kiraye daga wasu kungiyoyin Fulani da suka nuna bukatar a samar da babbar kungiya da za ta jagoranci sauran kananan kungiyoyi a fafutukar kare al’adun al’ummar Fulani a Nijeriya. Dalilan kafa kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore sun kuma hada da:
- Samar kungiyar da za ta hada kan dukkan sauran kungiyoyin Fulani tare da kare al’adun al’ummar Fulani a Nijeriya.
- Samar da mambobi masu girmama tare da mutunta shugabanni da sarakunan gargajiya na Fulani.
- Hada kai tare da tafiya tare da wasu kungiyoyi don ciyar da Nijeriya gaba.
- Tabbatar da hadin kai da tafiya tare da sauran wasu kungiyoyi.
- Taimaka wa manbobin kungiyar wajen dogaro da kai.
- Taimakawa wajen yada al’adun Fulani musamman yaren Fulani.
- Bayar da gudunmmawa wajen ayyukan ci gaba a garuruwan Fulani.
- Bayar da gudummawa wajen jin dadin al’ummar Fulani tare da mutunta juna.
- Tabbatar da kiwon dabbobi cikin lumana da zaman lafiya da kuma zaman lafiya tare da dukkan sauran al’ummonin Nijeriya.
Bababn kudurin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a karkashin shugabancin Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo shi ne hada kan al’umma Fulani don su zama tsintsiya madaurin ki daya.
Ba zaka taba samun mamban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore yana shiga harkokin rarrabuwan kai ba, domin cikakken ma’anar ‘Kautal Hore’ shi ne hadin kai tare da tafiya tare da dukkan al’ummar Fulani a dukkan sassan kasar nan.
Ta hanyar kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Shugaba Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo ya taimakawa al’ummar NIjeriya da dama ta hanyar biya musu kudin makaranta, kudin asibiti, gina makarantu, gina masallatai da kuma samar wa matasa aikin gwamnati a sassa daban-daban, ya kuma yi haka ne ba tare da nuna banbanci ba, a gare shi, shi shugaba ne ga kowa da kowa.
Ya kuma kafa kungiyar ‘yan sintiri mai suna ‘Nomad bigilante Group’ don kawo karshen yadda ake bata wa Fulkani suna. Ga kuma wasu dalilain da ya sa aka kafa kungiyar ‘yan sintirin.
Sun hada da samar da zaman lafiya a yankuna karkara, don taimaka wajen tattara bayanan sirri don kawo karshen sace-sacen shanu a yankuna karkara da kuma kare rayukan manoma da makiyaya. Sauran dalilan sun kuma hada da bukatar samar da tsaro ga gonaki da rugan kiwon shanu da wurin kiwo, haka kuma kungiyar tana samar da kiwon lafiyan da kuma kai agajin gaggawa a wuraren da aka samu wani iftila’i.
kungiyar ta samu nasara a bangarori da dama sun kuma ba mara da kunya wajen gudanar da ayyukan jin kai da kare dukiya da rayukan al’umma.
Ganin irin ayyukan alhairi da Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo yake yi wa al’umma da kuma irin gudummawar da ya bayar wajen kafa wannan gwmanatin muke ganin wannan kamun da aka yi masa tamkar wulakanci ne ga al’ummar Fulani ba na Nijeriya kadai ba har ma na duk duniya baki daya.
Yanzu fiye da makoi biyuj ke nan, muna kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta sako mana shugabanmu, musamman ganin har yanzu iyalai da masoyansa basu san halin da yake ciki ba har zuwa yanzu.
Amb. Suleiman shi ne sakataren watsa labarai na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore