Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya aike da sakon taya murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin ga shugaban kasar Xi jinping.
Mashawarci na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin yada labarai wanda kuma shi ne kakakinsa, Femi Adesina ne ya gabatar da sakon a shafin sada zumunta.
Shugaba Buhari, ya ce yana taya gwamnatin kasar Sin, da al’ummar Sinawa, cikinsu har da wadanda ke zaune a Nijeriya murna, tare da yi masu fatan alheri a sabuwar shekarar Zomo, kana ya jinjinawa nasarorin da Sin ta cimma karkashin shugabancin Xi Jinping.
Har ila yau, ya ce yana farin cikin ganin dangantaka da hadin gwiwar kasarsa da Sin na ci gaba da kasancewa mai karfi, inda Sin din ta kasance abokiyar huldarta mai karfi yayin da take kokarin samun ci gaba, musammam a fannonin ababen more rayuwa, da aikin gona da cinikayya da makamshi da tsaro.”
Ya ce duk da rashin kwanciyar hankali da duniya ta yi fama da shi a shekarar 2022, karkashin shugabancin Xi Jinping, kasar Sin ta ci gaba da yin kyakkywan tasiri ga harkokin duniya, da shaida nasarar gudanar da taron wakilan JKS karo na 20, wanda ya dora kasar bisa sabon tafarkin gina kasa ta zamani mai tsarin gurguzu ta kowacce fuska.
Ya ce yayin da al’ummar Sinawa ke murnar shiga sabuwar shekara, ya yi imanin shekarar Zomo za ta kawo dimbin ci gaba da kwanciyar hankali ga kasar Sin, tare da ci gaba da raya kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ga samun sabon ci gaba da nasara.