Shugaban Tanzania, John Magufuli, ya gana a jiya Juma’a, da mamban majalisar gudanarwar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, dake ziyara a Tanzania.
Shugaba John Magufuli, ya ce Sin ta samu gagarumar nasara ta fuskar ci gaban tattalin arziki kuma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, ta kasance ta moriyar juna. Ya ce a shirye Tanzania take, ta zurfafa dangantakarta da Sin da fadada fitar da kayayyaki zuwa kasar da kara jan hankalin Sinawa masu zuba jari.
A nasa bangaren, Wang Yi, ya ce Tanzania ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarta bayan ya hau karagar mulki a shekarar 2013. Kuma yayin ziyarar, shugaba Xi ya ce Sin za ta bi ka’idojin tsare gaskiya da samun sakamako a zahirance da tabbatar da aminci da kyakkyawar fata, yayin da take hulda da nahiyar.
A cewar Wang Yi, kasar Sin na goyon bayan kamfanoninta su zuba jari a Tanzania da fadada hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren samar da ababen more rayuwa da albarkatu da makamashi da noma da kiwo da samar da kayayyaki da magunguna da kiwon lafiya da sauran bangarori.
Har ila yau a jiya, ministan na Sin ya tattauana da takwaransa na Tanzania, Palamagamba Kabudi, inda suka kira taron manema labarai na hadin gwiwa. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)