Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, ya gana da mukaddashin shugaban majalisar dattawan Liberia, Nyonblee Karnga-Lawrence wadda ta zo kasar Sin domin halartar taron koli na mata na duniya.
Yayin ganawar, Zhao Leji, ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da Liberia wajen aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin biyu suka cimma da ma sakamakon taron koli na Beijing na FOCAC da kuma ci gaba da marawa juna baya kan manyan batutuwa da muradun kasashen da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da karfafa hadin kai da bayar da gudunmuwa ga gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya, dake iya jure kowanne yanayi.
Ya kara da cewa, a shirye majalisar wakilan jama’ar Sin ta ke ta zurfafa musaya a banagren harkokin doka da gogewa da takwararta ta Liberia, da karfafa musaya kan kare hakkin mata da muradunsu ta hanyoyin doka da samar da muhalli mai aminci na hadin gwiwa. (Fa’iza Mustapha)














