Yanzu dai ba labari ba ne cewa al’amura suna shirin kwabe wa tsarin rabon shugabancin jam’iyyar APC mai mulki, biyo bayan koma-bayan da jam’iyyar ta samu kan batun rarraba mukami na shiyya-shiyen a shugabancin majalisar ta 10 da jam’iyyar ta fitar a ranar Litinin da ta gabata.
Bisa la’akari da yadda lamarin ke kara kamari, zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a cikin jam’iyyar na gab da rugujewa a yayin da zababbun ‘yan majalisar da aka zaba su a karkashin inuwar jam’iyyar suka yi barazanar tayar da kayar baya idan ba a sake duba tsarin shiyya-shiyya mai cike da ce-ce-ku-ce ba daga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta kasa.
- Shugaban Tsimi Da Tanadi Ya Warware Mishkilar Dimbin Bashin Da Ake Bin Jihar Kaduna
- Zambia Ta Shirya Jan Hankalin Sinawa Masu Zuba Jari
Shugabancin jam’iyyar a hukumance ya tabbatar da amincewa da tsohon ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godwill Akpabio, (daga Jihar Akwa Ibom a kudu maso kudu) a matsayin shugaban majalisar dattawa, da Tajudeen Abbas (daga Jihar Kaduna a Arewa maso yamma) a matsayin shugaban majalisar wakilai.
‘Yan majalisar da suka fusata sun bayyana salon shiyya-shiyya mai cike da ce-ce-kuce a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar kuma bai dace da tsarin dimokuradiyya ba. Suna da ra’ayin cewa bai kamata jam’iyyar ta karkata zuwa yankin maimakon duba kananan shiyya ga daidaikun mutane.
Idan dai za a iya tunawa, wasu masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai da zababbun ‘yan majalisa da dama ne suka fara yi wa lamarin bore yayin ganawarsu da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdulahi Adamu a ranar Larabar da ta gabata.
Sun kuma yi barazana ga shugabancin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan kar su maimaituwa kuskuren 2015 idan jam’iyyar ta bar tsarin shiyyar da ta dage a kan shi ba. Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai a shekarar 2015 sun bijire wa zabin jam’iyya mai mulki tare da zabar nasu ‘yan takara masu zaman kansu a manyan mukamai a majalisun tarayya guda biyu.
Wadanda suka tsaya takarar shugaban majalisar wakilai da zababbun ‘yan majalia a taron sun kasance karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Hon. Idris Wase.
Wadanda suka tsaya a wurin taron sun hada da Hon. Yusuf Gagdi, Hon. Muktar Betara, Hon. Ahmed Jaha, Hon. Femi Bamishile, Hon. Abubakar Nakraba, Hon. Mariam Onuaha, Hon. Sani Jaji, Hon. Sada Soli da kuma Hon. Mariam Onuoha.
Hakazalika, a ranar Alhamis da ta gabata tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, da babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, da Sanata Osita Izunaso da Sanata Sani Musa suka mika takardar bore a lokacin wata ganawa da Adamu da sauran mambobin kwamitin gudanarwa, inda suka nuna rashin jin dadinsu kan tsarin shiyya-shiyya da jam’iyyar ta fitar.
Sun yi gargadin cewa jam’iyyun adawa na iya samun nasara idan ba a sake duba tsarin shiyya-shiyya da jam’iyyar ta fitar ba.
Yari ya ce Arewa za ta yanke shawara idan ba a sake duba yarjejeniyar shiyyar ba, yayin da Musa ya ce dole ne a gyara rashin adalcin da ke tattare da shirin shiyya-shiyya, inda Kalu ya sha alwashin za su kalubalanci tsarin shiyya-shiya da ake shirin yi.
Dangane da barazanar da kuma bacin ran da ya biyo bayan tsarin shiyyar, Adamu ya roki fusatattun sanatocin da suka kwantar da hankalinsu, yana mai cewa shugabannin APC za su sake duba tsarin shiyya. Ya yarda cewa ba a tuntubi ‘yan majalisar yadda ya kamata ba.
To sai dai kuma duk da cewa jam’iyya mai mulki na iya samun nasara a zauren majalisar dattawa, amma a majalisar wakilai lamarin ba haka yake ba, saboda jam’iyyun adawa ke da rinjayen a zauren majalisar.
Wani abin sha’awan shi ne, jam’iyyun adawa da suka hada da PDP, NNPP, SDP, LP da sauran su ne ke da rinjaye a majalisar da kujeru 180, yayin da APC ke da 178. Kujeru guda biyu ne ake jira, daya daga Akwa Ibom saura kuma daga jihohin Ondo.
Duk da cewa jam’iyyar ta amince da Abbas a matsayin kakakin majalisar wakilai, Muktar Betara, wanda ke wakiltar mazabar Biu/Bayo/Shani ta Jihar Borno, shi ne mutumin da zai iya lashe wannan mukami bisa irin farin jinin da yake samu a tsakanin takwarorinsa ‘yan majalisa.
Dan majalisar na Borno wanda ya bayyana kaduwarsa kan zaben da jam’iyyar ta yi na shugaban majalisar, ya ce babu wanda zai sa shi ya janye takararsa.
A ganawar da yayi da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a ranar Larabar da ta gabata, Betara ya ce babu wani lokacin da aka ware ga mukaman shugabanni majalisu guda biyu zuwa yanki daya.
Betara ya jaddada rashin amincewarsa da matakin na kakaba shugaban majalisar wakilai, yana mai cewa za su iya amince da wani dan takarar ne kawai da aka amince da shi bisa yarjejeniya.
Hakazalika, Gagdi ya yi kashedi game da kakaba shugabancin majalisar daga wajen zauren majalisa.
A cewarsa, “Muna da kudurin aniyar kare dimokuradiyya. Majalisar wakilai ita ce majalisar al’ummar Nijeriya. A lokacin da muka fara aiki gadan-gadan, babu shugabancin jam’iyyar da zai kasance a wurin. Mu za mu dukufa wajen gudanar da ayyukan yin doka”
A kwanakin baya ne wasu zababbun ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP, LP, NNPP da APC suka yi taro a Abuja, inda suka yanke shawarar cewa ba za su mutunta matakin da APC ta dauka na shiyya-shiyya ba, amma suna goyon bayan Betara.
Haka kuma sun yi nuni da cewa kasancewar zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya fito ne daga yankin Arewa maso gabas bai hana Betara ya zama shugaban majalisar wakilai ba idan aka yi la’akari da tarihinsa da gogewarsa da kuma ayyukansa a karo na hudu a zauren majalisa.
An fara zaben Betara ne a shekara ta 2007. A matsayinsa na shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, ya nuna himma, tsantseni da kwarewa a matsayinsa wanda ya rike mukamin mai gudanarwa da kuma kula da albarkatu na cikin tsarin kasafin kudi yana ba da gudummawa wajen bincikar ayyukan da suka dace a kan al’amurar kasafin kudi.
Betara ya gudanar da ayyuka a mazabarsa ta fuskar aiwatar da makilci nigari. Ya sami damar gudanar da dibin ayyuka don taimaka wa al’ummar mazabarsa wajen dakile musu matsalolin da suka addabe su.
Ayyukan da ya gudanar sun hada da gina kananan filayen wasanni har guda biyar na wucin-gadi a kananan hukumomin Biu, Bayo, Shani da Kwaya- kusar a Jihar Borno da gina cibiyar kula da cutar daji a Maiduguri da gina tituna samu nisan kilomita 80 a kananan hukumomin Biu, Bayo, Kwaya-kusar da Shani da gyarawa da gina sabbin ofisoshin ‘yansanda a kananan hukumomin Biu da Kwaya da gina gidajen zamani na jami’an DSS da sauran jami’an tsaro a kananan hukumomin Biu da Kwaya kusar da dai sauransu.
Zababben dan majalisar mai wakiltar mazabar Obudu/Obanliku/Bekwara na Jihar Kuros Ribas, Peter Akpanke na jam’iyyar PDP, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa na yankin kudu maso kudu bayan taron ya ce tsarin shiyya-shiyya na jam’iyya mai mulki ba zai haifar da da mai ido ba.
Ya ce, “Dukkanmu ba ’yan jam’iyyar APC ba ne, don haka duk abin da suka yanke ba zai zama mai tasiri a kanmu ba. Wannan shi ne shawarar jam’iyyarsu.
Idan za su iya shawo kan membobinsu, hakan yana da kyau a gare su. Amma ba su da yawa, mu ‘yan adawa mun fi yawa. Suna bukatar mu kafin su iya samar da shugaban majalisar wakilai. Mun san cewa ba duk ‘ya’yan jam’iyyar APC ba ne ke goyon bayan matakin da jam’iyyar ta dauka ba.
Yayin da jam’iyya mai mulki za ta bukaci a sake duba tsarin shiyya-shiyya, amma shugabannin jam’iyyar su na jiran zababben shugaban kasa wanda ba ya kasar ya tantance hanyar da za a bi. Duk wani abu da ba a yi nazari ba zai ga gwamnati mai shigowa ta fara kan hanyar da ba ta dace ba, wanda dole ne a kauce masa.