Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugabancin Nijeriya na daya daga cikin kalubale mafi tsanani a rayuwa.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata a cikin sakonsa na Sallah mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, inda ya jaddada cewa shugabanci na kunshe da hadin kai da goyon bayan dukkan ‘yan kasa.
Tsohon Shugaban kasar Nijeriya yana daya daga cikin kalubalen rayuwa mafi wuya a rayuwa, in ji Buhari.
Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su bai wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu cikakken goyon baya.
Ya kara da cewa, “Shugabanci aiki ne mai kalubale da ke bukatar sadaukarwa da goyon bayan ‘yan kasa,” in ji shi.
Buhari ya kuma yi wa Musulman Nijeriya barka da Sallah da kuma “wadanda suka yi aikin Hajji fatan yin ibada karbabbiya da kuma dawowa gida lafiya”.
Tsohon shugaban kasa haifaffen Katsina ya kammala wa’adin mulkinsa na wa’adi biyu na shekara takwas a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Buhari kuma shi ne shugaban mulkin soja na Nijeriya tsakanin Disamba 1983 zuwa Agusta 1985.