Kungiyar ‘ya’yan jam’iyyar PDP na yankin arewa ta tsakiya ta fara tattaunawa da shugabannin jam’iyyar PDP domin fitar da shugaban jam’iyyar na kasa daga yanki domin samun damar kammala wa’adin mulkin Dakta Iyorchia Ayu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta sanar da ranar gudanar da babban taron kwamitin zartarwa da ta tsara za a yi a ranakun 17 da 18 ga Afrilun 2024.
- An Gudanar Da Zaman Sakatarori Na Taron Kiyaye Tsaro Na SCO Karo Na 19
- Bayani A Kan Zakkar Shan Ruwa Da Sallar Idi
Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar a tsakanin shugabanni jam’iyyar a yankin ya yi nisa.
Wata majiya mai tushe ta ce, “Muna tsammanin yankin zai bayyana zabinsa kafin babban taron kwamitin zartarwa.”
Cikin mutanen da ake tsammanin za a fitar sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki daga Jihar Kwara da Sanata Gabriel Suswam wanda suka fito daga wuri daya da Ayu a Jihar Benuwai.
Haka kuma an bayyana cewa shugabannin jam’iyyar a yankin sun gana a Abuja domin gudanar da shirye-shiryen cimma wannan burin nasu.
Wadanda suka halarci ganawar sun hada da shugabannin jam’iyyar na jihohi shida da ke yankin arewa ta tsakiya ciki har da na Abuja da kuma sauran wakilai da aka zaba.
Sakamakon ganawar ya nuna cewa mahalarta tron sun amince shugabancin PDP ya tsaya a yankin arewa ta tsakiya domin kammala wa’adin mulkin Ayu, yayin mafi yawanci suka amince da cewa Damagum ya ci gaba da rike mukaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa.
Majiya a wurin taron ta bayyana cewa ana tsammanin gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang zai shirya taron shugabannin yankin domin tattauna yadda za a cimma samun wannan nasara.
Majiyar ta ce, “Da yake yanzu zaben 2023 ya shude, muna tsammanin shugabannin jam’iyyar za su yi abin da ya dace wajen sake fasalin jam’iyyarmu dpmin ta dawo kan hayyacinta.
“Lokacin da Ayu yake shugabancin jam’iyyar ya yi kokari sosai, shi ya sa mu mutanen yankin arewa na tsakiya muka hadu wuri guda tare da amincewa a maye gurbinsa daga cikinmu, saboda matsayar da aka cimma a 2023 har yanzu tana aiki. Tsarin mulkin jam’iyyarmu ya amince da haka.
“Mun gudanar da taro kan wannan matsalar. Idan za mu iya tunawa dai, shugabanninmu sun gudanar da ganawa a Abuja, bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.”
A dai mika shugabancin jam’iyyar PDP a yankin arewa ta tsakiya kafin zaben 2023, wanda Ayu ya zama shugabanta ba tare da wata hamayyya ba.
An dai zabi Ayu ne domin ya maye gurbin Prince Uche Secondus wanda aka cire daga mukaminsa bisa rawar da mai gidansa a siyasa ya taka kan lamarin.
Ya dai fuskanci matsin lamba daga wurin Wike Nyesom Wike shugaban gwamnonin PDP biyar da suka balle da ake kira G-5, tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na neman tikitin zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Bayan samun takaddama mai zafi, daga karshe dai an cire Ayu a matsayin shugaban PDP, inda aka sa mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa, Illiya Damagum dan asalin Jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas a matsayin mukaddashin shugaba tun daga ranar 28 ga Maris na 2023.
A yanzu haka dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da Damagum yake jagoranta yana shan matsin lamba kan gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.