Manyan daraktocin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) daga yankin Arewa maso Yamma sun gudanar da taro a Kaduna domin tsara sabbin dabaru na yaƙi da matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Taron, wanda ya gudana a ofishin rundunar DSS da ke kan titin Maj.-Gen. Muhammadu Buhari Way, ya tattaro shugabanni daga jihohin Kano, da Kaduna, da Katsina, da Kebbi, da Jigawa, da Sokoto, da Zamfara, tare da wakilai daga FCT, da Neja, da Filato. Haka kuma, an samu halartar manyan jami’an tsaro daga rundunonin Sojoji, da Ƴansanda, da Kwastam, da FRSC da NSCDC.
- DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta
- DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
A lokacin buɗe taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, wanda Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Sule Shuaibu (SAN) ya wakilta, ya jaddada muhimmancin haɗin kai mai dogaro da bayanan sirri wajen magance matsalolin tsaro. Ya ce “haɗin kai mai tushe a kan bayanan sirri shi ne mafi tasiri wajen murƙushe barazanar tsaro a Arewa maso Yamma da ƙasa baki ɗaya.” Gwamnan ya yabawa DSS bisa rawar da take takawa wajen kare dimokuraɗiyya da hana rikice-rikicen da ka iya zama barazana ga ƙasa.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, wanda ya halarci taron, ya yabawa DSS bisa ci gaba da haɗin kai da masarautu wajen warware rikice-rikicen cikin al’umma. Ya bayyana cewa masarautar ta warware fiye da ƙararraki 2,000 cikin shekaru biyu ta hanyar hanyoyin da DSS ta taimaka wajen samarwa. “Mun rage cunkoson kotuna kuma mun tabbatar da adalci a matakin ƙasa. Mafi kyau a cire shugabannin gargajiya marasa nagarta tun farko kafin su cutar da jama’a,” in ji shi.
A nasa jawabin, wakilin GOC na Runduna ta 1 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Mohammed Kana, ya bayyana cewa bayanan sirri daga DSS sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin Sojoji a yaƙin da suke yi da ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji a Arewa maso Yamma. “Taimakon bayanan sirri daga DSS ne ke bai wa Sojoji damar samun nasara a fagen fama,” in ji shi.
Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali.














