Shugabannin duniya na ci gaba da taya Xi Jinping murna, bisa zaben da aka yi masa na ci gaba da kasancewa shugaban jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
A sakonsa, shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya ce a shirye yake ya hada hannu da bangaren kasar Sin wajen daukaka dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi domin cimma burika da muradun al’ummominsu.
Shi kuwa shugaban kasar Kenya William Ruto, cewa ya yi, kasarsa za ta ci gaba da tabbatar da dangantaka da hadin gwiwa ta kut-da-kut da kasar Sin, kamar yadda kasashen biyu suka yi bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu, shekaru 60 da suka gabata.
A nasa bangare, shugaban Zimbabwe Emmersn Mnangagwa, ya ce karkashin shugabancin Xi Jinping mai cike da hikima, kasar Sin ta samu ci gaban tattalin arziki kuma ta shiga wani sabon babi na ci gaba.
Shi ma shugaban hukumar Tarayyar Afrika (AU) Moussa Faki Mahamat, ba a bar shi a baya ba, inda ya ce nahiyar Afrika za ta ci gaba da dagewa wajen karfafa hadin gwiwarta da kasar Sin. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp