Shugaban kasa Muhammad Buhari da takawaransa na Jamhuriyar Nijar, Muhammad Bazun za su bude gasar karatun Alkur’ani Mai tsaki karo na (37) gobe Juma’a a jihar Zamfara.Â
Gasar kamar yadda wakilinmu ya nakalto cewa Jami’ar Usman Danfodiyo ce ke shiryawa da gabatarwa a duk Shekara.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin hadimin gwamnan Jihar Zamfara a bangaren yada labarai, Hon. Zailani Bappa, inda yake cewa tunin shirye-shiryen suka yi nisa wajen amsar bakwancin gasar.
Bappa wanda ke magana a madadin shugaban kwamitin Yada labarai na kwamitin gasar kuma kwamishinan yada labarai na Jihar Zamfara, Hon. Ibrahim Magaji Dosara, ya ce, shugabannin Kasa Nijeriya da Nijar ne za su jagoranci bude gasar
Inda Kuma kuma Gwamnan Jihar Borno Baba Gana Umara Zulum zai kasance shugaban taron, kana masu Martaba Sarkin Musulmi da Shehun Borno ne iyayan taron.
Ya kara da cewa gasar za a yi ta ne na tsawon mako guda inda za a tantance hazikan da za su wakilci kasar Nijeriya zuwa gasar ta duniya da za a gudanar da ita kasa Saudiyya.
Akan haka ne kwamitin gasar ke neman goyan bayan al’ummar Jihar Zamfara don ganin an yi taron lafiya an kammala lafiya.
Kwamishinan ya kuma bada tabbacin cewa Gwamnatin jihar ta yi tsare-tsaren da suka dace wajen ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara.