Game da abubuwan dake da nasaba da kasar Sin dake cikin rahoton tsaron kasa na shekarar 2022 da ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta wallafa a kwanakin nan, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya bayyana Jumma’ar nan cewa, wannan wani tsohon tunani ne na yakin cacar baka da kuma rashin kan gado ne.
Don haka, kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka, da ya yi fatali da tunanin yakin cacar baka, da kuma kara kaimi don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da ma shiyya-shiyya. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp