Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya zargi Amurka da yada karairayi, cewa wai kasar Sin na taimakawa Rasha da makamai a rikicin ta da Ukraine.
Geng Shuang, wanda ya yi tsokacin a jiya Juma’a, yayin zaman kwamitin tsaron MDD da aka yi, don nazartar batutuwan da suka shafi tallafin makamai ga Ukraine, inda ya ce ko kadan Sin ba za ta amince da wannan zargi ba.
- Sin: A Bara Darajar Cinikayya Tsakanin Kasashen Shiyya Karkashin RCEP Ta Kai Dala Triliyan 5.6
- Mataimakin Shugaban Brazil: Sin Ta Nuna Babban Misali A Fannin Yaki Da Fatara Da Bunkasa Fasahohi
Geng Shuang ya kuma jaddada cewa, ba Sin ce ta kirkiri rikicin Ukraine ba, kuma ba ta da hannu cikin gudanar sa. Har kullum Sin na nacewa manufar shawo kan rikicin ta hanyar siyasa, da kayyade dukkanin kayayyakin aikin soji da ake iya amfani da su a harkokin fararen hula, kuma ko kadan Sin ba ta samar da makamai ga ko wane bangare na rikicin.
Jami’in ya kara da cewa, dukkanin harkokin raya tattalin arziki da cinikayya dake gudana tsakanin Sin da Rasha, ana gudanar da su ne bisa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, da sauran tsare tsaren kasuwanni, kuma ba su da wata manufa ta illata wani sashe na daban, ko karya dokokin kasa da kasa.
Hasali ma a cewar jami’in, bayan barkewar rikicin Rasha da Ukraine, ba a taba dakatar da hada hadar cinikayya tsakanin Amurka da Rasha ba. Sai dai abun takaici a irin wannan yanayi, Amurka na ci gaba da zargin kasar Sin kan halastattun huldodin cinikayyar ta da Rasha, kawai da nufin kawar da zargi daga kan ta, da kaucewa daukar alhakin laifin ta.
Daga nan sai Geng Shuang ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta dakatar da batawa Sin suna ta fakewa da batun Ukraine, ta dakatar da kakaba takunkumai na kashin kai, da kokarin murkushe kamfanonin Sin. Ya ce har kullum, Sin na fatan Amurka za ta yi kokarin ba da kyakkyawar gudumawa, wajen ganin an kawo karshen yaki, da maido da zaman lafiya cikin hanzari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)