Kasar Sin ta fitar da shirin gaggauta gina ingantaccen tsarin ayyukan lissafin na’urori masu kwakwalwa mai karfi na kasa, wanda zai hade damar samar da hidimomin manyan lissafi daga na’urori masu kwakwalwa.
Shirin zai ingiza aiwatar da tsarin kasar na “Tattara bayanai daga gabas da tasaftawa a yammacin kasa”, da gaggauta gina hadakar na’urori masu kwakwalwa masu matukar karfin sarrafa bayanai na kasa.
- Jirgin Ruwa Mai Binciken Teku Na Farko Na Kasar Sin Ya Gwada Yin Aiki Cikin Nasara
- Sin Ta yi Nasarar Harba Tare Da Gwada Taurarin Dan Adam Na C Karo Na 24
Shirin wanda hukumomin kasar 5 suka fitar, ciki har da hukumar kula da bayanan kwamfuta ta kasar da kwamitin tsara manufofin samar da ci gaba da aiwatar da sauye sauye na kasar, na da nufin zaburar da ci gaban tattalin arzikin kasa mai kunshe da managarcin karfin ayyukan na’urori masu kwakwalwa, ta yadda hakan zai ba da gagarumar gudummawa ta gina karfin kasar a fannin tsaron yanar gizo, da tattalin arziki na dijital.
Shirin ya yi hasashen cewa, ya zuwa karshen shekarar 2025, Sin za ta samar da cikakken tsarin ayyukan ababen more rayuwa masu nasaba da na’urori masu kwakwalwa mafiya karfin lissafi. Kana adadin sabon mizanin karfin lissafin na’urori masu kwakwalwa na kasar zai zarce kaso 60 bisa dari, kuma karfin ayyukansu zai samar da sauki da rahusa, yayin da fasahohin da ake bukata domin cin gajiya daga hakan za su kasance masu tsaro da inganci.
Bugu da kari, shirin ya tanadi gudanar da ayyukan tsara karfin lissafin na’urori masu kwakwalwa tsakanin gabashi da tsakiya da yammacin kasar Sin, tare da yayata hade gajiyar karfin lissafin na’urorin, da bayanai da tsarin ayyukan manhajoji. Har ila yau, za a tsara da bunkasa, da wanzar da tsaron karfin aikin na’urori masu kwakwalwa yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)