Tun daga yau Alhamis 18 ga wata, aka fara aiwatar da manufar kafa hidimar “kwastam mai zaman kanta, a duk fadin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin” a hukumance, da zummar kafa tashar ciniki mai ’yanci mafi girma a duniya, wadda za ta saukaka shigowar kayayyakin kasashen ketare cikin kasar Sin, da habaka nau’ikan kayayyakin da aka yafewa harajin kwastam, gami da karin matakai da za su kyautata muhallin kasuwanci.
Kafofin watsa labaru na kasashe daban daban, suna kallon wannan mataki da kasar Sin ta dauka a matsayin mai shaida yunkurinta, na raya ciniki cikin ’yanci, da kara bude kofa ga kasashen ketare, yayin da ake fuskantar bazuwar ra’ayin kariyar ciniki a duniya.
Bisa shirin da aka gabatar, an mai da tsibirin Hainan na kasar Sin, wanda fadinsa ya kai fiye da muraba’in kilomita dubu 30, wani yanki mai ka’idojin kwastam na musamman, da nufin ragewa, ko soke haraji, da saukaka zirga-zirga ko musayar kayayyaki, da kudi, da mutane, gami da alkaluma.
Dangane da lamarin, wasu al’ummun kasashen Afirka, sun fayyace mahangarsu, inda masanin ilimin tattalin arziki dan kasar Zambiya Yusuf Dodia, ya ce shugaba Xi Jinping na kasar Sin, yana son ganin an dinke sassan wasu shiyyoyi, don ba da damar raya harkar cinikin kasa da kasa yadda ake bukata. Kana matakin da aka dauka a tsibirin Hainan a wannan karo, zai saukaka ayyukan shigar da kayayyaki cikin kasar Sin, da fitar da kayan kasar zuwa kasashen waje.
A nasa bangare, babban editan gidan rediyon Capital FM na kasar Kenya Bernard Momanyi, ya ce matakin kaddamar da manufar kafa hidimar kwastam mai zaman kanta a tsibirin Hainan, tana da matukar ma’ana ga kasar Sin, gami da duk duniya baki daya. A ganinsa, tabbas yadda kasar Sin take kara bude kofarta ga kasashen waje cikin inganci, da sa kaimi ga gudanar cinikayyar kasa da kasa, da dukufa wajen gina tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, za su amfani daukacin al’ummun duniya. (Bello Wang)














